Garin neman kiba: Banki ya fece da kudin kwastomomi yayin da suke jiran rancen miliyoyi

Garin neman kiba: Banki ya fece da kudin kwastomomi yayin da suke jiran rancen miliyoyi

  • Yanzu haka dai hukumomin ‘yan sanda a jihar Ondo na ci gaba da neman ma’aikatan wani banki a jihar Ogun bayan korafe-korafen da abokan huldansa suka shiga
  • Abokan huldar, wadanda gama gari ne da kananan 'yan kasuwa, sun firgita lokacin da suka nemi ma'aikatan bankin suka rasa
  • An an wayi gari ne an ga shugaban bankin da ma'aikatansu sun bar gari tare da rufe ofishin banki, lamarin da ya gigita kwastomomin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Wasu mazauna gari sun kai kokensu ofishin ‘yan sanda na Mowe da ke jihar Ogun, bisa zargin cewa wani karamin banki ya sace musu kudi.

Bankin ya yi alkawarin bai wa kwastomominsa rancen kudi bayan ajiye wasu adadi na kudi a asusu amma ma'aikata da bankin suka yi batan dabo bayan karbe dan abin da ke hannun 'yan kasuwan.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

Yadda banki ya guduwa da kwastomomi kudi
An so a ci banza: Banki ya fece da kudin kwastomomi yayin da suke jiran rancen miliyoyi | Hoto: Neil Thomas
Asali: Getty Images

Amma mazauna yankin sun yi mamakin ganin bankin ya rufe ofishinsa ba tare da mayar da kudaden da aka karba ba kana ba tare da ba da rancen da ake tsammani ba.

Wadanda abin ya shafa sun bayyana bakin cikinsu

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Funmilayo Adebayo ta shaidawa jaridar Punch cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mu kusan uku ne muka N50,000 tare wanda muka ba su saboda muna son a ba mu rancen N150,000. Na sha wahala lokacin da nake da ciki don nemo kudin da na ba su. Yanzu da na kwanta na ke bukata, na yi asarar kudin.”

Wata da abin ya shafa, Nike, ta bayyana cewa ta bukaci a ba ta rancen N200,000 sannan ta ba da N24,000 ga bankin.

“Nawa ba kome ba ne idan aka kwatanta da abin da wasu suka ba su. Akwai wata mata da na gani tana sharbar kuka a Lotto jiya saboda ta basu Naira 200,000 akan rancen naira miliyan daya."

Kara karanta wannan

Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a wata jiha

Morenike Ajayi, ta nemi rancen kudi N200,000 domin bunkasa sana’arta ta sayar da abinci.

Ta ce:

“Na kwallafa rai kan wannan kudi tun tunda na dauki sauran kudaden da ke cikin asusuna, na ci bashin karin daga wajen wani kawa ta da zimmar da zarar na karbi rancen, zan biya ta in saka sauran a cikin kasuwanci na. Yanzu, wadannan hatsabiban sun lalata duk wani shiri na. A ina zan fara?”

Abimbola Oyeyemi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'u a zabe

A wani labarin, jaridar Leadership ta ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki na shirin siyan kuri’u domin lashe zaben shugaban kasa a zaben 2023 da za a yi nan gaba kadan.

Shugaban riko na PDP Amb. Umar Damagun, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya bukaci ‘yan Najeriya da su karbi katin zabe na dindindin (PVC), a matsayin wani mataki na kalubalantar tsare-tsaren APC.

Kara karanta wannan

Ondo: Masu bauta da aka ceto daga gidan kasa sun ki yadda su komawa iyalansu, sun ce sun fi son wurin fasto

Damagun wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai, ya ce: “Abin da suke tunani shi ne a 2023, za su zo su saye ku su ci gaba da bautar da ku, su bar ku a gida, su rufe makarantunku, su ba ku damar zama 'yan bindiga. Ya rage naku yanzu ku fita can ku nemi PVC dinku."

Asali: Legit.ng

Online view pixel