Ondo: Masu bauta da aka ceto daga gidan kasa sun ki yadda su komawa iyalansu, sun ce sun fi son wurin fasto

Ondo: Masu bauta da aka ceto daga gidan kasa sun ki yadda su komawa iyalansu, sun ce sun fi son wurin fasto

  • An yi karamar dirama a ofishin CID na 'yan sandan jihar Ondo da wasu daga cikin wadanda fasto ya garkame a gidan kasan cocinsa dake jihar
  • An gano cewa, wasu daga ciki sun ce ba zasu koma cikin dangisnu ba, sai dai su koma wurin faston, lamarin da yasa ake zargin ya asircesu
  • A ranar Juma'a ne 'yan sanda suka ceto mutum 77 da fasto ya garkame na tsawon sati uku suna jiran bayyana Yesu Almasihu

Ondo - Wasu daga cikin masu bauta 77 da aka ceto daga gidan kasa na cocin jihar Ondo sun ki yarda su koma ga iyalansu.

An yadda masu bauta da suka hada da kananan yara, suka shaki isklar 'yanci daga gidan kasan da cocin The Whole Bible Believers wanda aka fi sani da cocin Ondo dake yankin Valentino a birnin Ondo.

Kara karanta wannan

Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

Masu bauta a Ondo
Ondo: Masu bauta da aka ceto daga gidan kasa sun ki yadda su komawa iyalansu, sun ce sun fi son wurin fasto. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin iyayen da 'ya'yansu suka je wurin babu izininsu ne suka kai kara ofishin 'yan sanda, Channels Tv ta ruwaito.

An gano cewa cocin tana yin wani shiri ne na tsawon kwanaki bakwai yayin da 'yan sanda suka tsinkayi farfajiyarta a ranar Juma'a. Mutum saba'in da bakwai da suka hada da kananan yara 26, matasa takwas da manya 43 ne aka ceto bayan sun kwashe wurin makonni uku a kulle.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan ceto su, iyaye da 'yan uwan wadanda lamarin ya ritsa dasu sun dinga ziyartar ofishin CID na 'yan sanda dake Akure domin daukan 'yan uwansu.

Sai dai kuma, an yi wata karamar dirama a ranar Litinin yayin da wasu daga ciki suka ki bin danginsu inda suka jaddada cewa zasu cigaba da zama da faston.

Amma a tattaunawar da aka yi da wasu daga cikin danginsu, sun ce suna zargin faston da asirce musu 'yan uwa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

Kwamishinan harkokin mata ta jihar Ondo, Dr Juliana Osadahun, ta yi bayanin matsayar gwamnati kan lamarin.

Kamar yadda tace, gwamnati zata gana da 'yan sanda da 'yan uwan wadanda lamarin ya shafa domin samun gamsasshen bayani sannan ta san matakin dauka.

Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance

A wani labari na daban, Rabaran Andrew Abayomi, daya daga cikin fastocin majami'ar Katolika ta St Francis ta titin Owa-luwa a Owo da ke jihar Ondo, ya labarta yadda aka kai wa majami'ar farmaki.

Daily Trust ta ruwaito yadda masu bauta da dama suka rasa rayukansu yayin da 'yan ta'adda suka tada bom a majami'ar a safiyar Lahadi.

A wata tattaunawa da BBC harshen Yarbanci, faston ya ce wadanda ake zargin 'yan ta'addan sun shiga ne yayin da ake dab da kammala bautar ranar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel