Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'u a zabe

Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'u a zabe

  • Jam'iyyar PDP ta zargi takwararta ta APC mai mulki d shirya bautar da 'yan Najeriya a bayan zaben 2023
  • Ta bayyana haka ne tare da zargin akwai shiryen-shiryen APC na sayen kuri'u a zaben 2023 mai zuwa nan gaba
  • PDP ta kuma ta'allaka munanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sakamakon sakaci irin na mulkin APC

Najeriya - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki na shirin siyan kuri’u domin lashe zaben shugaban kasa a zaben 2023 da za a yi nan gaba kadan.

Shugaban riko na PDP Amb. Umar Damagun, wanda ya bayyana hakan a jiya, ya bukaci ‘yan Najeriya da su karbi katin zabe na dindindin (PVC), a matsayin wani mataki na kalubalantar tsare-tsaren APC.

Kara karanta wannan

Saba alkawari: Ta karewa APC a Sokoto, 'yan kasuwa sun yi watsi da ita sun koma PDP

APC za ta saye kuri'u a 2023, inji PDP
Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'un a zabe | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Damagun wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai, ya ce:

“Abin da suke tunani shi ne a 2023, za su zo su saye ku su ci gaba da bautar da ku, su bar ku a gida, su rufe makarantunku, su ba ku damar zama 'yan bindiga. Ya rage naku yanzu ku fita can ku nemi PVC dinku."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake shawartar matasa da su nemi katunan zabe domin su canza gwamnatin da ke kan mulki, Damagun ya ce:

“Kamar yadda kuke gani a kasar nan, yawancin matasanmu a yau ba su da aiki. Menene dalili? Rashin shugabanci na gari. Ta yaya za mu canza hakan?
"Ku je ku ku nemi PVC dinku. Ku fita ku wayar da kan mutane, su fito kwan su da kwarkwata. Duk wannan yajin aikin ASUU da muke gani, rashin aikin yi, ‘yan bindiga da sauransu, duk sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari. Ta yaya za ku canza rashin shugabanci na gari, ya rage na ku ku yi amfani da kuri’unku ku yi aiki a yanzu.”

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Akwatunan zabe 748 sun kone a inda tsageru suka kona ofishin INEC

'Yan Najeriya na cikin kaskanci saboda APC, shugaban matasan PDP

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban matasan jam’iyyar na kasa, Mohammed Suleiman, ya bayyana cewa al’ummar kasar na a matsayi mafi kaskanci, karkashin shugabancin jam’iyyar APC, rahoton Independent.

Ya ce:

“Matasan kasarmu sun fahimci abin da zai biyo baya. A kan haka ne muke kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su fito su karbi PVC dinsu domin wannan ne kawai makamin da za a iya tube su, wadannan dodanni da ke makale a kujerun mulki."

Gabanin 2023: ‘Yan kasuwan Sokoto sun bar APC sun kama PDP bisa saba alkawuran APC

A wnai labarin, 'yan kasuwa a Sokoto sun fice daga APC zuwa PDP saboda rashin cika alkawura da APC ta yi wa Kungiyar matasan ‘yan kasuwan jihar Sokoto.

Sun koma PDP, jam'iyya mai mulki a jihar domin marawa tafiyar jam'iyyar baya a zabuka da ke tafe a 2023.

Kara karanta wannan

Zabe: INEC ta shiga damuwa kan yadda ba a karbar katunan zabe gabanin 2023

Rahoton Daily Trust ya ce, ’yan kasuwar da suka yi tir da kasancewarsu a jam’iyyar APC sun yi ficewarsu daga cikinta ne a cibiyar tarihi da ke Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel