Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

  • Mai ba Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta shawara kan tsaro, Olorogun Samuel Oghotomo, ya sha da kyar a hannun yan bindiga
  • Maharan sun dana masa tarko ne a hanyar Oguname-Ophorigbala-Ovwor da ke karamar hukumar Ughelli South
  • Yan bindigar sun wawure makudan kudade da muhimman kayayyaki na miliyoyin naira bayan sun gaza samun nasarar hallaka shi

Delta - Babban mai ba gwamnan jihar Delta shawara kan harkokin tsaro, Olorogun Samuel Oghotomo, ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga a yankin Ovwor da ke karamar hukumar Ughelli South ta jihar, jaridar Independent ta rahoto.

Oghotomo, wanda ya bayyana halin da ya shiga ga manema labarai, ya ce yan bindigar wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun toshe hanyar da zai bi na old Oguname-Ophorigbala-Ovwor da misalin karfe 9:15 na daren Litinin.

Kara karanta wannan

Garin neman kiba: Banki ya fece da kudin kwastomomi garin neman rancen miliyoyi

Gwamna Ifeanyi Okowa
Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

Ya ci gaba da bayanin cewa da ya lura da shingen, sai ya yi gaggawan danna motarsa zuwa baya.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Yayin da motar ta koma baya, sai yan bindigar suka rufa mun baya kafin motar ta tsaya cak, sannan na gaggauta fita daga ciki inda na tsere cikin daji.
“Da suka gano cewa ina tsere masu, sai suka fara harbi ba kakkautawa ta inda nake amma dai na sha da kyar. Sun tsere da kudade da wasu muhimman kayayyaki na miliyoyin naira.”

Da aka tuntube shi, shugaban karamar hukumar Ughelli South, Hon. Cif Richard Kofi, ya tabbatar da lamarin.

Ya kuma bayyana cewa an dauki matakan da suka dace domin hana sake afkuwar irin haka a gaba, rahoton Daily Post.

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

Kara karanta wannan

Rikici: Wasu sun ta da zaune tsaye, sun kashe mai gadi, sun kone gidan mai a wata jiha

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu limaman cocin Katolika biyu a jihar Edo.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan masu garkuwa da mutane sun kashe wani limamin Katolika mai suna Christopher Odia a jihar.

A ranar Asabar, 2 ga watan Yuli ne aka yi garkuwa da limaman, Rev fr. Uboh Philemon na St. Joseph Retreat Centre da Rev. Fr. Udoh Peter na St. Patrick’s Catholic Church, Uromi dukkansu a Ugbokha, karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel