Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo

  • Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu limaman cocin Katolika guda biyu a jihar Benin a ranar Asabar
  • Maharan sun sace Rev fr. Uboh Philemon da Rev. Fr. Udo Peter na a hanyar Benin-Auchi suna dawowa daga wani taro
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tura wata tawagar jami'an tsaro don kamo masu laifin da kuma ceto malaman addinin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Edo - Channels TV ta rahoto cewa wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu limaman cocin Katolika biyu a jihar Edo.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan masu garkuwa da mutane sun kashe wani limamin Katolika mai suna Christopher Odia a jihar.

Limaman Katolika
Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin Katolika 2 a jihar Edo Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A ranar Asabar, 2 ga watan Yuli ne aka yi garkuwa da limaman, Rev fr. Uboh Philemon na St. Joseph Retreat Centre da Rev. Fr. Udoh Peter na St. Patrick’s Catholic Church, Uromi dukkansu a Ugbokha, karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

An sace su ne a hanyarsu ta komawa gidajensu bayan halartan wani taro a Benin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Maharan sun farmake su ne a hanyar Benin-Auchi tsakanin Ekhor da yankin Irukpen sannan suka tsere da su daji.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce yan sanda sun samu labarin garkuwa da malaman addinin biyu ta hannun DOP din Ugboha.

Nwabuzor ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Abutu Yaro, ya tura wata tawagar yan sanda don farautar yan bindigar da ceto mutanen.

Yan Bindiga Sun Kai Wa Yan Sanda Hari, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

A wani labarin mun ji cewa mutane na cikin fargaba a babban birnin jihar Enugu a yayin da wasu yan bindiga suka kai hari shingen binciken yan sanda suka kashe biyu cikinsu da wasu.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Tana Tantance Ministoci 7 da Buhari ya Mika Sunayensu

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da safe a Gariki, MTD a karamar hukumar Enugu South a babban birnin jihar kamar yadda The Punch ta rahoto.

A lokacin hada wannan rahoton, majiyoyi sun shaida wa wakilan Punch cewa ana nan ana harbe-harbe a iska a yayin da mutane ke tserewa don neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel