Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban babban asibiti a jihar Zamfara

Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban babban asibiti a jihar Zamfara

  • Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban babban asibitin Dansadau a jihar Zamfara
  • Maharan sun sace Mansur Muhammad ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuni a Mashayar Zaki da ke hanyar Dansadau-Magami a jihar Zamfara
  • Shugaban kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar, Dr Mannir Bature ya tabbatar da batun sace Muhammad

Zamfara - Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban babban asibitin Dansadau, Dr Mansur Muhammad, kamar yadda gidan talbijin na Channels ta rahoto.

Garin Dansadau na a karamar hukumar Maru kimanin kilo mita 100 daga Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

Taswirar Zamfara
Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban babban asibiti a jihar Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa dauke da sa hannunsa, shugaban kungiyar likitocin Najeriya ta NMA reshen Zamfara, Dr Mannir Bature, ya ce sun kadu matuka da samun labarin sace Dr Muhammad.

Nigerian Tribune ta nakalto Dr Bature yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Cike da kaduwa kungiyar NMA Zamfara ta samu rahoton garkuwa da Shugaban babban asibitin Dansadau, Dr Mansur Muhammad.
“Mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, 2022 a Mashayar zaki hanyar Dansadau - Magami da ke jihar Zamfara.
“Muna umurtan mambobinmu da su saka shi da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a addu’o’inmu yayin da kungiyar ke aiki tare da sauran hukumomi masu alaka don tabbatar da sakinsa kan lokaci cikin koshin lafiya.”

Hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane na kara kamari a Zamfara.

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ce umarnin da ta bai wa mazauna kuma farar hula na mallakar bindigogi don kare kansu, ba wai ana nufin kowa ya mallaki bindiga ne sakaka ba.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, inji rahoton Daily Trust.

A sabon matakin da gwamnatin jihar ta dauka kan 'yan ta'adda, ta ce za ta aike da fam 500 na ba da lasisin mallakar bindiga ga masarautun jihar 19.

Asali: Legit.ng

Online view pixel