'An haife shi 1958, ya fara karatu 1959' Sabbin tambayoyin da suka fito kan takardun mukaddashin CJN

'An haife shi 1958, ya fara karatu 1959' Sabbin tambayoyin da suka fito kan takardun mukaddashin CJN

  • Bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rantsar da muƙaddashin CJN, wasu alamun tanbayoyi sun biyo baya game da takardunsa
  • A takardun sabon Alkalin Alkalai, Olukayode Ariwoola, ya nuna cewa bai cika shekara ɗaya ba ya fara zuwa makarantar Firamare
  • Haka nan Alkalan arewa a Kotun Koli sun nuna damuwa game da rashin lafiyar da yake fama da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A ranar Litinin, bayan murabus din Ibrahim Tanko Muhammad, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin muƙaddashin shugaban Alƙalan Najeriya (CJN).

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa ana tsammanin Ariwoola ya cigaba da rike muƙamin har zuwa lokacin da majalisar shari'a ta ƙasa (NJC) da majalisar tarayya zasu tabbatar da shi.

Yayin rantsuwar kama aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja, muƙaddashin CJN ya yi rantsuwa zai yi biyayya ga gwamnatin tarayya da kuma kare kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban alkalan Najeriya Tanko Muhammad

Muƙaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola.
'An haife shi 1958, ya fara karatu 1959' Sabbin tambayoyin da suka fito kan takardun mukaddashin CJN Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Sai dai a yanzu wasu sabbin tambayoyi sun taso game da takardun karatun Ariwoola kuma musamman ranar da ya fara karatu a makaranta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An haife shi 1958 kuma ya fara zuwa makaranta 1959

An haifi Ariwoola a garin Iseyin jihar Oyo, ranar 22 ga watan Agusta, 1958. Takardunsa sun nuna cewa ya fara zuwa makarantar Firamare a garin su tun kafin ya cika shekara ɗaya a 1959.

Ya shafe shekara 8 a makarantar kafin ya kammala a shekarar 1967, daga nan ya wuce makarantar Muslim Modern School a cikin garin daga 1968 zuwa 1969.

Ya kammala karatunsa na Sakandire a makarantar Ansar-Ud-Deen high school, da ke yankin Saki a jihar Oyo.

Ya samu shaidar kammala karatun Digiri a fannin shari'a a Jami'ar Ife (wacce yanzu ake kiranta Jami'ar Obafemi Awolowo) a 1980. Shekara ɗaya bayan haka ya zama cikakken lauya kuma ya samu aiki a Kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa da ya Kamata a Sani Game da Sabon CJN Olukayode

Rashin lafiya

Kafin rantsar da shi, wasu majiyoyi daga cikin Kotun Koli sun shaida wa jaridar cewa Alƙalan arewa ba su goyon bayan naɗa shi bisa hujjar cewa ana zargin yana fama da rashin lafiya.

Suna ganin cewa rashin lafiyar da Ariwoola ke fama da ita ka iya shafar aikinsa a matsayin shugaban Kotun Ƙoli kamar yadda ta faru da tsohon CJN, Tanko Muhammad.

A wani labarin na daban kuma Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare

Bayan kwashe kwanaki 62 a garkame, Babbar Kotun jihar Ribas karkashin jagorancin Mai Shari'a Chinwendu Nworgu ta amince da buƙatar ba da Belin ɗan majalisar wakilan tarayya, Honorabul Farah Dagogo.

Ledership ta ruwaito cewa Dagogo,wanda ya nemi takarar gwamna a jam'iyyar Peoples Democratic Party wato PDP , na fuskantar shari'a ne kan zargin aikata babban laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel