Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sace sabon DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sace sabon DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu matsala yayin da 'yan bindiga suka sace DPO a wani yankin jihar Kaduna
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da aka tura shi yankin Birnin Gwari na jihar kuma ya yi yunkurin kama aiki
  • Sai dai, rundunar 'yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ana ci gaba da bincike kan tushen batun

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

An yi garkuwa da wani sabon jami’in ‘yan sanda (DPO) da aka tura zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa, DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama aikinsa lokacin da aka sace shi.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Yadda 'yan bindiga suka sace DPO a Kaduna
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sace sabon DPO a kan hanyarsa ta kama aiki a Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ba a bayyana ko jami'in na tafiya shi kadai a cikin motarsa ba ko tare da wasu ba lokacin da aka yi awon gaba da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu dai 'yan sanda ba su mayar da martani ko kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan sace jami'in ba, rahoton Ripples Nigeria.

Da aka tuntubi Mohammed Jalinge, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya ce, “Zan binciki lamarin kuma in sanar daku.”

Sojoji sun kakkabe mafakar IPOB/ESN, sun kwato makamai masu hadari

A wani labarin rundunonin tsaron Najeriya sun yi nasarar fatattakar mafakar 'yan ta'addan IPOB a jihar Anambra ta yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da tsohon mukaddan soji SK Usman ya yada, sanye da hannun Brig. Gen. Onyema Nwachuku ta bayyana irin arangamar da jami'an na sojin kasa, sama, DSS, 'yan sanda da sauransu suka yi, lamarin da ya kai kwato masu muggan makamai masu hadarin gaske.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kama wanda ya harbe tsohon hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami'ai sun yi amfani da nakiya wajen fito da tsagerun daga mafakarsu, kuma an yi nasarar kassara karfinsu a sansanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel