Da dumi-dumi: An kama daya daga cikin wadanda suka harbe hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

Da dumi-dumi: An kama daya daga cikin wadanda suka harbe hadimin Jonathan, Ahmad Gulak

  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta gabatar da wasu 'yan ta'adda, ta ce ta kama daya daga wadanda suka kashe Ahmad Gulak
  • Wannan na zuwa ne shekara guda da 'yan kai bayan hallaka jigon na jam'iyyar APC a yayin wata ziyara a Imo
  • Rahoton da muka samo ya kuma bayyana cewa, an gabatar da wasu da ake zargi da tada hankalin jama'ar jihar ta Imo

Jihar Imo - Hukumomin ‘yan sanda a jihar Imo sun ce sun kama daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe jigo a jam’iyyar APC, Ahmed Gulak, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Mista Mike Abattam, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Imo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni a Owerri, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 a jihar Borno

An kama makashin Ahmad Gulak
Da dumi-dumi: An kama daya daga wadanda suka harbe hadimin Jonathan, Ahmad Gulak | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wanda ake zargin mai suna Anosike Chimobi daga karamar hukumar Ahiazu Mbaise (LGA) ta jihar an kama shi ne shekara guda bayan mutuwar Gulak.

Yadda aka kashe Gulak a bara

Wasu gungun tsagerun ‘yan bindiga sun kashe Gulak, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne a ranar 30 ga Mayu, 2021, yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Imo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni sun ce an bi sawun sa ne daga dakin otal din da ya sauka zuwa inda aka kashe shi a kusa da Umueze Obiangwu a karamar hukumar Ngor-Okpala, kusa da titin filin jirgin sama na Sam Mbakwe a Owerri.

Da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu, Abattam ya ce Chimobi ya na kan idon hukumar tun bayan kashe Gulak a bara.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere ne a wani artabu tsakanin jami’an ‘yan sanda da ‘yan tawagarsu a Aboh Mbaise jim kadan bayan kashe jigon na jam’iyyar APC inda aka kashe biyar daga cikin wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

Chimobi ya tofa albarkacin bakinsa

Chimobi, wanda shi ma ya zanta da manema labarai, ya yi ikirarin cewa shi direban bas ne na kasuwanci ba mamban kungiyar 'yan ta'adda ba.

Ya ce wadanda suka kashe Gulak sun neme shi ne domin ya dauke su a motarsa ​​kuma ya yi yunkurin yin turjiya, amma daga baya ya yarda bayan sun yi barazanar kashe shi.

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya tuka 'yan ta'addan zuwa wurin tare da tare motar Gulak da ke kan hanyarta ta zuwa filin jirgin sama.

A cewarsa, sun harbe jigon na APC ne bayan ya bijirewa bukatar ‘yan bindigar na ya sauko daga motar.

Chimobi ya bayyana cewa, daga baya maharan sun ci karo da tawagar jami’an tsaro inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi kan motar har ta kama da wuta.

Sauran wadanda aka kama

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce ‘yan sanda sun kuma kama wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban na addabar al’umomin Imo.

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama akwai ‘yan kungiyar da suka kona gidan shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, inji rahoton The Nation.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin da ‘yan sandan suka gabatar sun hada da bindigogi daban-daban, layu iri-iri, da maciji mai rai da dai sauransu.

'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

A bara kunji cewa, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Gulak, jigo a jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a daren ranar Asabar yayin da yan bindigan suka kashe shi.

A cewar jaridar Tribune, tsohon abokinsa da suka yi makaranta tare, Dr Umar Ado ne ya bada sanarwar rasuwarsa a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel