Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 a jihar Borno

Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 a jihar Borno

  • Jam'iyyar NNPP a jihar Borno ta bayyana kwarin gwiwar cin zabe a babban zaben 2023 mai zuwa a matakai daban-daban
  • Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban jam'iyyar na Borno, inda ya bayyana adadin mambobin NNPP a Borno
  • A cewarsa, yanzu jam'iyyar na ci gaba da wayar da kan masu kada kuri'a, kuma yana da yakinin taka rawa a zaben

Maiduguri, Borno - Jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) ta yi ikirarin cewa sama da mutane miliyan biyu ne a jihar Borno suka yi rajista a matsayin mambobin jam’iyyar.

Mista Mohammed Mustafa, shugaban NNPP a jihar ya yi wannan ikirarin ne a Maiduguri ranar Lahadi. PM News ta ruwaito.

Al'ummar Borno dai, bisa kiyasi sun kai akalla kimanin mutum miliyan 5.86.

Yadda NNPP ta samu karbuwa a jihar Borno, inji shugabanta
Kayan marmari: Jam'iyyar su Kwankwaso NNPP ta samu mutane miliyan 2 jihar Borno | Hoto: dailynews24.ng
Asali: UGC

A cewar Mustafa jam’iyyar tana da farin jini sosai a Borno kuma yanzu haka ta shirya tsayin daka don jawo sauran 'yan jam’iyyun siyasa cikinta tare da tunzura sauran jam'iyyu a zaben 2023 a jihar.

Kara karanta wannan

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta rahoto daga majiya yana cewa:

“Mun fitar da ‘yan takara a dukkan mutakai a jihar Borno kuma muna da tsare-tsare tun daga unguwanni har zuwa jiha, muna wayar da kan masu kada kuri'u.
“Baya ga dan takarar shugaban kasa Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso, muna da dan takarar gwamna, ‘yan takarar sanata uku, ’yan majalisar wakilai 10 da ’yan majalisar jiha 28 da za mu zaba a Borno.
“Muna shirin ba wa wasu mamaki da karfin mu na mambobi sama da miliyan biyu da magoya baya.
"Muna sa ido kan zabukan 2023 da cikakken kwarin gwiwa da fatan samun nasara da yardar Allah."

Ya yabawa INEC kan kara wa’adin rijistar katin zabe na dindindin (PVC) da ke gudana a halin yanzu, sannan ya bukaci al’ummar Borno musamman matasa da su shiga a dama dasu.

Kara karanta wannan

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

A kalamansa:

"Abu ne mai ban tsoro amma ina so in yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri'a wadanda a yanzu sun kara wayewa da su dauki himma don su je su yi rajista domin su taka rawar gani wajen zaben shugabannin da suke so."

Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

A wani labarin, Amb Ginika Tor ta yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su yi kuskuren zaben jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Wakiliyar ta jihar Enugu a hukumar da’a ta tarayya ta ce jam’iyyar PDP ba ta cancanci kuri’un kabilun Igbo ba, saboda kin amincewar jam’iyyar na ba da tikitin takarar shugaban kasa a yankin kudu maso gabas, inji rahoton jaridar The Nation.

Ta ce a maimakon goyon bayan Atiku tare da kada masa kuri'u, ya kamata dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shahara ya kuma mamaye kuri'un yankin.

Kara karanta wannan

Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel