Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

- An kashe tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Barista Ahmed Gulak

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka halaka hadimin na Jonathan a Owerri

- Ya taso daga Owerri yana kan hanyarsa na komawa babban birnin tarayya Abuje ne wannan mummunan lamarin ya faru

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Gulak, jigo a jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a daren ranar Asabar yayin da yan bindigan suka kashe shi.

DUBA WANNAN: Bahaushen Da Ya Riƙe Amanan Bayarabe Tsawon Shekaru 30 Ya Sha Yabo

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar jaridar Tribune, tsohon abokinsa da suka yi makaranta tare, Dr Umar Ado ne ya bada sanarwar rasuwarsa a ranar Lahadi.

KU KARANTA: An Rufe Makarantar Sakandare Ta Mata Saboda Tsoron 'Iskokai' a Kwara

"Yanzu na tabbatar da abin bakin cikin da ya faru na mutuwar abokina kuma wanda muka yi makaranta tare, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, tsohon mataimaki na musamman ga Shugaba Goodluck Jonathan, Barista Ahmed Ali Gulak wanda aka ce yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe shi a Owerri, jihar Imo," a cewar Umar Ardo.

Ya taba ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa a yayin rikicin shugabancin jam'iyyar a shekarar 2016.

Gulak ya taba rikie mukamin shugaban kwamitin jam'iyyar APC da ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar gwamna a jihar Imo.

Ya bace bayan isarsa jihar domin sanya ido kan yadda za a yi zaben a Oktoban 2018.

Daga baya ya ce an 'sace' shi ne tare da sauran mambobin kwamitinsa kuma an bashi Dalla miliyan 2 domin ya yi magudi a zaben.

Ya kuma yi ikirari cewa a wannan lokacin, Rochas Okorocha, gwamnan Imo ya tilastawa mambobin kwamitin zaben su ayyana Uche Nwosu, dan takarar da ya ke goyon baya a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.

Daga bisani kwamitin ayyuka na kasa, NWC, na APC ta soke zaben bayan an sanar da Nwosu a matsayin wanda ya lashe zabe.

Jonathan ya sallame shi a matsayin masharcinsa kan harkokin siyasa a Afrilun 2014.

Ba a bada dalilin sallamarsa ba amma ana zargin yana katsalandan a harkokin jam'iyyar PDP a jihohi.

A lokacin, ya yi rikici da Godswill Akpabio, gwamnan jihar Akwa Ibom na wannan lokacin kuma shugaban gwamnonin PDP.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164