Buba Marwa ya na neman tona asirin ‘Yan siyasa, NDLEA ta cafke masu harkar kwayoyi

Buba Marwa ya na neman tona asirin ‘Yan siyasa, NDLEA ta cafke masu harkar kwayoyi

  • Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce NDLEA ta kama wasu ‘yan siyasa dauke da mugayen kwayoyi
  • Hukumar ta yi nasarar aika wani ‘dan siyasa zuwa gidan kurkuku bayan an same shi da wannan laifi
  • Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce su na fama da wasu matsaloli duk da irin kokarin da yake yi a ofis

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban hukumar NDLEA mai yaki da masu amfani da safarar miyagu na kasa, Buba Marwa, ya ce sun damke wasu ‘yan siyasa da kwayoyi.

Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya tabbatarwa Duniya cewa NDLEA ta yi ram da ‘yan siyasa da kwayoyi.

Kamar yadda aka fitar da rahoto a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni 2022, Buba Marwa ya nuna takaicinsa a game da yadda ya samu cikas a wajen aikinsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Shugaban hukumar NDLEA yake cewa bai yi nasara a yunkurin da ya nemi ya kawo na ganin an yi wa duk jami’in gwamnati gwaji kafin ya shiga ofis ba.

NDLEA ta yi koyi da Kano

A cewar Janar Marwa, NDLEA ta aro wannan tsaro ne daga jihar Kano, inda ake yi wa duk wasu ‘yan APC gwajin kwayoyi kafin a ba su mukami a gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buba Marwa
Shugaban NDLEA, Buba Marwa a Aso Villa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

"Mun kama ‘yan siyasan da ko su na rike da mukamai a yanzu, ko sun yi ritaya. Kwanan nan aka daure wani daga cikinsu a gidan yari a Legas"

Dabarar da ake yi a Najeriya

“An daure shi yana kokarin ya yi safarar kilo daya. Watakila zai yi amfani da shi wajen takara.”
“Kamar yadda ku ka sani, masu dillacin kwayoyi su na shiga siyasa, su na ba ‘yan takara gudumuwa domin a taba doka idan sun ci zabe.”

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

Akwai matsala har gobe

Da yake bayanin yadda kula da tsofaffin ‘yan kwaya, The Cable ta rahoto Marwa yana cewa duk wuraren kula da tubabbun mashaya kwaya sun lalace.

A cewarsa, akwai dinbin mutane da ke so su daina wannan muguwar harkar, amma sun gagara.

Marwa ya ce a halin yanzu cibiyoyi 11 rak ake da su na kula da wadanda suke neman yin ban kwana da miyagun kwayoyi, a maimakon uku a duk jiha.

Ekweremadu ya shiga uku

Ku na da labari cewa Sanata Ike Ekweremadu da Mai dakinsa Beatrice sun shiga matsala a hannun jami’an Birtaniya a kokarin yi wa diyarsu dashen koda.

‘Dan majalisar na Najeriya ya kinkimi karamin yaro zuwa kasar waje da nufin ya diyarsa kodarsa. A karshe an kama su a bisa zargin yaron bai kai shekara 18 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel