An tono shekarun yaron da Sanata Ekweremadu suka kai Ingila domin cire masa koda

An tono shekarun yaron da Sanata Ekweremadu suka kai Ingila domin cire masa koda

  • Sanata Ike Ekweremadu da Mai dakinsa Beatrice sun shiga matsala a hannun jami’an Birtaniya
  • ‘Dan majalisar na Najeriya ya kinkimi karamin yaro zuwa kasar waje da nufin ya diyarsa kodarsa
  • Ana zargin wannan yaro bai kai shekara 18 ba, amma hujjoji su na nuni har ya kusa kai shekara 22

England - An samu karin bayani a game da matashin da Sanata Ike Ekweremadu da Beatrice Ekweremadu suka dauka zuwa Ingila domin a cire masa koda.

Idan za a tuna, an yi niyyar wannan Bawan Allah zai bada kodarsa daya domin dasawa ‘diyar tsohon mataimakin shugaban dattawan wanda ba ta da lafiya.

Rahoton da aka samu daga The Cable ya tabbatar da cewa sunan wannan yaro; Ukpo Nwamini David.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya jajantawa Sanatan da aka kama da zargin safarar sassan jikin mutum a Birtaniya

Mista Ukpo Nwamini David ne aka yi alkwari da shi zai ba Sonia Ekweremadu koda. Amma da aka iso asibitin Birtaniya da za ayi aikin, sai lamarin ya canza.

Shekarar Ukpo Nwamini David 15?

Hukumomin Birtaniya su na zargin cewa shekarar Ukpo David 15 a Duniya, don haka bai kai munzalin da zai dauki matakin kyautar da bangaren jikinsa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma kuma rahotanni sun nuna lallai akwai ta-cewa a game da shekarun wannan matashi.

Ukpo Nwamini David
Takardun fasfon Ukpo Nwamini David Hoto: www.kossyderrickent.com
Asali: UGC

Ko da ‘yan sandan Ingila su na ikirarin shekarunsa 15 da haihuwa, bayanan da aka samu daga fasfonsa na fita kasar waje ya tabbatar da akasin wannan bayani.

A fafson Ukpo, an fahimci shekarunsa 21 domin kuwa an haife shi a ranar 12 ga watan Oktoban 2000. Yanzu shekarunsa 21 da watanni takwas da ‘yan kwanaki.

Kara karanta wannan

Ekweremadu na hanyar zuwa Turkiyya sayan sabuwar koda muka kwamushe shi, Lauyoyi

Haka zalika da aka duba takardar BVN na rajistar banki da Ukpo ya yi, an tabbatar da ya haura 15. Wadannan hujjoji sun nuna matashin ya zarce shekara 18 tun tuni.

...An sabawa dokar Turai

Legit.ng ta fahimci Ukpo Nwamini David yana gara-ramba ne a Legas, bai da wurin zama. Sanatan ya yi masa alkawarin canza rayuwarsa idan ya bada kodarsa.

Sai dai babban laifi ne a Ingila a dauki wani mutumi daga kasar waje, ya zo asibiti da nufin kurum ya bada kyauta ko ya saida wani bangaren jikinsa kamar yadda aka yi.

Ekweremadu ya sanar da hukuma?

Ku na da labari a shekarar 2021, Ike Ekweremadu ya sanar da hukumomi game da dashen kodar da za ayi wa 'Diyarsa a wata wasika da ya aikawa ofishin jakadanci.

Ana zargin cewa Sanata Ekweremadu wanda tun 2003 yake majalisar Najeriya, ya nemo wani yaro da bai da kowa a Duniya, aka yi masa takardun bogi zuwa Ingila.

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

Asali: Legit.ng

Online view pixel