Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

  • Doyin Okupe ya tabbatar da cewa ana bakin kokarin ganin Jam’iyyar LP da NNPP sun hada-kai
  • Watakila Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso za su tsaya takarar shugabancin Najeriya tare a 2023
  • Jagororin LP sun bayyana cewa ba a gama magana a kan wanda zai rike tuta idan an dunkule ba

Abuja - Doyin Okupe ya bayyana cewa ‘Dan takararsu na LP, Peter Obi da kuma Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP su na tattauna a kan hadin-kai.

Vanguard ta rahoto Dr. Doyin Okupe yana mai cewa wadannan manyan ‘yan siyasa biyu za su yi kokarin ganin sun tsaya takara tare a zaben shugaban kasa.

Dr. Okupe yake cewa jam’iyyarsu da kuma ta NNPP sun amince su kawo sabon tsari, amma ya ce har yanzu bangarorin ba su kai ga fitar da ‘dan takara ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shahararren 'Dan kasuwan Najeriya ya ba takarar Peter Obi kwarin gwiwa

Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce abin da suke kokarin yi shi ne a karkare magana kafin wa’adin 17 ga watan Yuli da hukumar INEC ta tsaida.

“An yi zama sau biyu da ni a wurare dabam-dabam a kan maganar. Zan iya fada maka kai-tsaye, na yi magana da Rabiu Kwankwaso a kan wannan batu.”
“Har yanzu ba a samu matsaya a kan wanda zai zama ‘dan takarar shugaban kasa tsakanin Arewa da Kudu ba, domin kowa ya hakikance a kan shi ya dace.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Doyin Okupe

Peter Obi da Kwankwaso
Kwankwaso da Peter Obi su na tsere Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Da Okupe ya zanta da Vanguard a jiya, ya ce har yanzu Mai gidansa ya na magana da Kwankwaso, idan an dace, su biyu za su dunkule tare.

Abure da Tanko sun tabbatar da haka

Haka zalika Mai magana da yawun bakin jam’iyyar LP na kasa, Julius Abure ya tabbatar da cewa su da NNPP su na kokarin shirya babban taron dangi.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

Sakataren yaa labarai na LP, Dr Yinusa Tanko ya ce maganar wanda zai rike tikiti idan an dunkule yana hannun Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Lissafi zai canza - Jigon NNPP

Da yake bayani a shafinsa, sakataren kudi na jam’iyyar NNPP a Kano, Aliyu Isa Aliyu ya ce nan da watanni masu zuwa, NNPP da LP za su rikita siyasa.

Dr. Aliyu Isa Aliyu yake cewa kafin zaben 2023, za a canza ra’ayin masu zaben ‘yan takara.

Obi Cubana ya bi Obi

Dazu kun samu rahoto cewa shugaban kamfanin Cubana Group, Mista Obinna Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana, ya shiga sahun 'Yan Obedients.

Obi Cubana ya yi magana yana mai nuna goyon bayansa ga ‘dan takarar nan na LP watau Peter Obi. A cewar 'dan kasuwan, Obi kadai zai iya gyara Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel