2023: 'Wasu Mutane Da Ba A Sanansu Ba' Ne Suka Sace Takardun Karatuna, Tinubu Ya Fada Wa INEC

2023: 'Wasu Mutane Da Ba A Sanansu Ba' Ne Suka Sace Takardun Karatuna, Tinubu Ya Fada Wa INEC

  • Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya fada wa hukumar zabe INEC cewa wasu da bai san ko su wanene ba sun sace takardun karatunsa
  • Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin cike fom na takarar shugaban kasa wacce ya mika wa INEC gabanin zaben 2023 inda aka kawai karatunsa na Jami'ar Chicago ya saka babu frimare da sakandare
  • Sai dai, bisa alamu wannan bayanin da Tinubu ya rubuta a takardar zaben na 2023 ya sha banban da abin da ya fada wa INEC yayin zaben 1999 inda ya ambaci sunan makarantun da ya yi frimare da sakandare

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya shaidawa hukumar zabe mai zaman kanta cewa wasu mutane da bai sani ba suka sace masa takardun karatunsa lokacin ya yi hijirar dole zuwa kasar waje, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon gwamnan na Jihar Legas, ya bayyana hakan cikin takardan rantsuwa da ya gabatarwa INEC yayin cike fom din takarar shugaban kasa cewa ya 'tafi hijirar dole daga Octoban 1994 zuwa Octoban 1999 kuma da na dawo sai na gano wasu da ban sani ba sun sace kayayaki na har da takardan shaidan karatu da ake nema a sakin layi na 3.'

Bola Tinunu
2023: 'Wasu Mutane Da Ba A Sanansu Ba' Ne Suka Sace Takardun Karatuna, Tinubu Ya Fada Wa INEC. @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da Tinubu ya tsallake bayanai na karatunsa na sakandare da frimare yayin cike fom din na INEC, ya ce ya yi karatu a Jami'ar Chicago tsakanin 1972 da 1976 inda ya yi digiri a bangaren Nazarin Tattalin Arzikin.

Ya kuma ce yana da digiri a bangaren Kasuwanci da Gudanar da Mulki da kuma satifiket na aiki a matsayin Akanta.

Wannan ya saba da bayanan da Tinubu ya bada a 1999 yayin takarar gwamna a Legas

Wasikar ta Tinubu, bisa alamu ta ci karo da bayanan da ya bayar a zaben da suka gabata a 1999, a lokacin da ya yi takara kuma ya ci zaben gwamnan Jihas Legas.

Ya yi ikirarin ya yi karatun firmare da sakandare.

A lokacin, ya yi ikirarin ya yi karatun frimare a St Paul Children’s Home School, Ibadan, daga 1958 zuwa 1964; yayin da ya yi karatun sakandare a Government College Ibadan (GCI), daga 1965 zuwa 1968.

Ya yi ikirarin daga Ibadan ya kuma tafi Richard Daley College, Chicago, daga 1969 zuwa 1971.

Sai dai, fitaccen lauyan Najeriya marigayi Gani Fawehinmi ya kallubalance takardun karatun yana mai cewa na bogi ne.

An yi shari'a da Fawehinmi har zuwa kotun koli, inda aka yi watsi da karar saboda kuskure na tsarin shigar da kara amma ba don rashin hujja ba.

A fom dinsa, dan takarar shugaban kasa na PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya gabatar da digirin digir-gir a matsayin karatu mafi girma da ya yi.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel