Jerin zargin rashin gaskiya da ke jikin ‘Yan takaran 2023, Atiku Abubakar da Bola Tinubu

Jerin zargin rashin gaskiya da ke jikin ‘Yan takaran 2023, Atiku Abubakar da Bola Tinubu

  • Bloomberg ta kasar waje, ta bi manyan ‘yan takaran shugaban kasa a zaben 2023, tayi bincike a kan su
  • Jaridar ta yi wa Bola Tinubu da Atiku Abubakar binciken kwa-kwaf a kan zargin da ake yi masu
  • Ko da har yau ba a kama wadannan ‘yan siyasa ba, akwai tulin zargi masu karfi a kan wuyansu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A wani rahoto da ya fito a makon nan, Bloomberg ta kakkabo zargin da ke wuyan ‘dan takaran APC, Bola Tinubu da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Wannan dogon rahoto ya fallasa cewa an taba zargin Bola Tinubu a Amurka da laifin karkatar da kudin da aka samu daga harkar kwayoyi a shekarun 1990s.

Manyan masu neman karbar mulkin Najeriya a 2023, Atiku mai shekara 75 da Tinubu ‘dan shekara 70, sun sha bam-bam da shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

Tinubu yana ikirarin ya samu kudinsa ne tun kafin ya shiga siyasa, shi ma Atiku yana fakewa da aikin kwastam, amma duk ana zargin sun amfana da gwamnati.

Shi kuma Atiku Abubakar da zai yi takara a PDP yana da kashin shigo da makudan Daloli daga kasar Amurka a lokacin yana mataimakin shugaban Najeriya.

Haka zalika ana tunanin akwai hannun Atiku a laifin da ya yi sanadiyyar daure wani ‘dan majalisar Amurka. Har yau babu wanda ya tuhume shi a kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

Harajin jihar Legas

Ana zargin cewa Tinubu yana da ta-cewa a kamfanin Alpha Beta Consulting LLP da aka ba kwangilar karbar harajin Lehas, yana samun makudan biliyoyi.

Mai magana da yawun bakin tsohon gwamnan ya musanya wannan magana. Sai dai wannan zargi ya yi karfi, har an bukaci EFCC ta binciki lamarin a baya.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

An taba kai Tinubu kotu?

A Yulin 1993, gwamnatin Amurka ta shigar da karar Bola Tinubu a kotu (lokacin yana Sanata), ta nemi karbe kudin asusun wani akawun da ya bude a garin Chicago.

Bincike ya nuna ‘dan siyasar ya taba zuba $1.8m a asusun, daga baya ya dauke kudin zuwa wani banki. A karshe sai da ya biya $460000 kafin sauran kudinsa su fito.

Hadimansa su na cewa binciken da aka yi a baya, ya wanke Mai gidansa daga wadannan zargin.

Badakalar Siemens a Amurka

Kusan sai a zaben 2019 ne aka cire takunkumin da ke kan Atiku Abubakar na hana shi zuwa Amurka a dalilin zargin da ake yi masa na hannu a wata badakala.

A 2010 kwamitin majalisar dattawan Amurka ya gano a cikin matan Atiku akwai wanda ta taimaka masa wajen boye kudin da sun kai Dala miliyan 40 a kasar.

Daga cikin wannan kudi ne aka ba kamfanin Siemens AG cin hancin fam Dala miliyan 1.7. A dalilin haka aka yankewa William Jefferson dauri na shekaru 13.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

NNPP da LP za su hada-kai

A gefe guda kuma, an ji cewa ana ta yin taro iri-iri domin ganin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun dawo karkashin inuwa daya a zaben shugaban kasa a 2023.

Doyin Okupe ya yi magana a kan wa zai zama ‘dan takara ko mataimaki, yayin da kwanaki 20 rak su ka rage a wa'adin da hukumar zabe na INEC ta ba jam'iyyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel