Miyagun ‘Yan bindiga sun shiga Kaduna, sun sace Matar Soja da wasu Bayin Allah cikin dare

Miyagun ‘Yan bindiga sun shiga Kaduna, sun sace Matar Soja da wasu Bayin Allah cikin dare

  • ‘Yan bindiga sun dura unguwar Millennium City da ke garin Kaduna, sun yi gaba da mutane shida
  • A wadanda aka dauka har da matar wani jami’in soja da aka shiga unguwar a lokacin ba ya gida
  • Mazauna yankin sun ce an shiga wani gida an dauki mai gidan da matarsa da masu yi masu aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - A daren Larabar nan, 21 ga watan Yuni 2022, wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi awon gaba da mutane bakwai a garin Kaduna.

Jaridar Vanguard ta ce miyagun sun dura unguwar Millennium City a jihar Kaduna, suka dauke mutane a unguwannin Keke ‘A’ da Keke ‘B’ da ke yankin.

A cikin wadanda aka dauka a yammacin ranar Talatar har da matar wani babban jami’in sojan kasa.

Kara karanta wannan

Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto

Har zuwa lokacin da ake tattara rahoton, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, bai yi magana a game da harin ba.

Karfe 11:00 sai ga 'yan bindiga

Amma dai mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindiga sun duro masu da kimanin karfe 11:00 na dare a jiya, suka dauke Bayin Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar mazauna unguwar, ‘yan bindigan sun shafe kimanin sa’a guda su na harbe-harbe. Kafin jami’an tsaro su kawo agaji, an dauke mutum uku a Keke 'A'.

Millennium City
Millennium City a Kaduna Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Kamar yadda mu ka samu rahoto, wadanda suka yi wannan aiki sun hari wani katafaren gida ne na wani soja. A lokacin shi bai nan, sai suka sace mai dakinsa.

Karamar yarinya ta tsira

Haka zalika mazaunan unguwar sun ce ‘yan bindigan sun shiga gidan makwabcinsa, suka dauki wani magidanci tare da diyarsa mai shekara takwas a Duniya.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

Bayan mahaifiyar yarinyar ta rika tsala ihu cikin dare, ‘yan bindigan sun ajiye mata diyarta. Daga nan kuma suka shiga buda wuta domin tsoratar da al'umma.

Ana haka ne kuma sai wadannan mutane suka ci karo da wani magidanci da bai san abin da yake faruwa ba, yana kokarin shiga gidansa, suka yi tafiyarsu.

A Keke ‘B’ kuwa, an dauke wani magidanci tare da matarsa da wasu ‘yan mata biyu da ke yi masu aiki. Wani mazaunin wannan yanki ya ce da kyar shi ya sha.

An kama makamai a K/Riba

Dazu kun ji labari asirin wasu miyagu ya tonu yayin da wani Direba da ya yi lodin kayan hada bama-bamai ya nemi ya tserewa jami'an sojoji a Kuros Riba.

Wata sanarwa daga Hedikwatar tsaro ta ce Jami’ain tsaron sun budawa wannan mota wuta, a karshe kuwa aka gano ta dauko alburushi da ruwan bam ne.

Kara karanta wannan

Karfin hali: ‘Yan sanda sun cafke wasu mutane 6 da ake zargin ‘yan fashin banki ne

Asali: Legit.ng

Online view pixel