Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto

Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto

  • Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa, an hallaka 'yan sanda shida yayin artabu da 'yan bindiga
  • Wannan ya faru ne yayin da 'yan bindigan suka yi wa motocin mahajjata kwanton bauna a jihar Sokoto
  • Yanzu dai an dage tashin jirgin mahajjatan, kana an saka wani sabon lokaci domin tafiyarsu zuwa Makkah

Sokoto - Shida daga cikin ‘yan sandan mobal da suka yi artabu da ‘yan bindiga a lokacin da suka kai wa ayarin mahajjata hari a Sokoto sun mutu a kan aikinsu.

A baya rahotanni sun bayyana yadda maniyyata aikin hajji da ke kan hanyar zuwa Sakkwato gabanin tashin jirgi zuwa kasa mai tsarki na Makkah suka gamu da tasgaro daga gungun 'yan bindiga a Gundumi.

An tattaro cewa an dawo da dukkan mahajjatan da ke shirin zuwa fadar Sarkin Gobir Isa ba tare da jin rauni ba.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

Yadda aka shirya sace mahajjata a Sokoto
Ganau: 'Yan bindiga sun bindige 'yan sanda 6 a yunkurin sace mahajjata a Sokoto | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Amma wani mazaunin garin Isa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust, cewa ‘yan ta’addan sun kashe ‘yan sanda shida.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“’Yan bindigar sun yi wa ayarin motocin da ke karkashin 'yan sandan mobal kwanton bauna. Jami’an da ke gaba sun yi artabu da ‘yan bindigar, kuma hakan ne ya sa mahajjatan suka tsere yayin da motocinsu suka koma zuwa Isa.”

An kuma tattaro cewa lamarin ya tilastawa hukumar jin dadin alhazai ta jihar dage tashin jirgin zuwa ranar Laraba saboda tun da farko an umarce su da ya tashi da karfe 7:30 na safiyar ranar Talata.

Wakilin jaridar ya kuma tabbatar da cewa tuni maniyyatan sun isa Sokoto, suna jiran tashin su.

Mai taimaka wa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, wanda ya tabbatar da harin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce jami’an gwamnati sun tarbi mahajjatan a babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

Da aka tuntubi mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce ba a yi masa bayani a hukumance ba game da mutuwar abokan aikinsa amma wata majiya ta ‘yan sanda ta shaida wa Daily Trust cewa an kashe jami’an.

Hajj 2022: Mutum biyu daga cikin maniyyata aikin Hajji sun rasu kafin tashin Jirginsu

A wani labarin, mahajjata biyu daga yankin ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Yakubu Abdulsamad da Haruna Suleiman sun rasa rayuwarsu kafin zuwan ranar tashinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa mhajjatan sun rasu ne ranar Lahadi da Litinin, kafin zuwan ranar tashin su zuwa ƙasa mai tsarki.

Jami'in dake kula da Mahajjatan ƙaramar hukumar, Aminu Surajo, wanda ya sanar da rasuwar su, ya ce tuni aka musu Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel