Jami’an Sojoji sun kama wata mota dankare da kayan makamai makil a Najeriya

Jami’an Sojoji sun kama wata mota dankare da kayan makamai makil a Najeriya

  • Rundunar sojojin Najeriya sun ce sun ci karo da wata mota da ta kinkimo tulin miyagun makamai
  • Motar ta biyo ta gaban Dakarun Sojoji don haka aka nemi a tsaida direban, amma ya ki tsayawa
  • Nan take aka budawa motar wuta, da aka bincika sai ga ta ta dauko bama-bamai, harsahi da khaki

Cross River - Rundunar sojojin Najeriya sun bada sanarwar kama wata mota da ta dauko makamai. Wannan lamarin ya faru ne a jihar Kuros Riba.

A wata sanarwa da ta fito a ranar Laraba, 22 ga watan Yuni 2022, an fahimci sojojin 13 Brigade da ke karkashin dakarun 82 Div ne suka yi wannan kokarin.

Jaridar Vanguard ta ce jami’an tsaron kasar sun samu makaman ne a wata mota kirar Toyota Camry mai lambar garin Jalingo a jihar Taraba (JAL 492 AA.)

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Motar ta na kokarin wucewa zuwa kauyen Utanga daga yankin tsaunukan Obudu a Kuros Riba.

Sanarwar da ya fito daga Hedikwatar sojojin kasa ya tabbatar da cewa sojoji sun yi kokarin tare wannan mota, amma sai direban ya ki tsayawa, ya zura a guje.

Makamai
Kayan da Sojoji suka karbe Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar da aka fitar

“Taurin kan direban ya tursasawa sojojin suka budewa tayoyin motar wuta, suka hana ta tafiya.”
“Da aka yi bincike da kyau, an gano cewa motar ta na dauke da kayan bam-bamai na IED 72, ruwan bam 121, casbi 200 na harsahin NATO mai mita 7.62.”

Haka zalika an kuma samu zagaye 82 na casbin wani harsashi na musamman mai tsawon mita 7.62

“Sauran kayan da aka samu a motar sun hada da khaki da kuma kayan sojoji.”

- Hedikwatar Sojoji

Jaridar ta ke cewa sanarwar ta yi kira ga jama’a su ba jami’an sojoji hadin-kan da ake bukata ta hanyar taimaka masu da bayanan da za su taimakawa aikinsu.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun yi farin ciki, an tsinci gawawwakin ‘yan ta’adda jibge a cikin rafi

Idan sojoji su na samun irin wadannan bayanai, za a magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.

An yi hira da Buhari

Ku na da labari cewa Gwamnatin Tarayya ta ce karin kufin fetur zai sa mutane su kara tagayyara, shiyasa aka hakura da maganar janye tallafin mai a bara.

An rahoto Muhammadu Buhari ya na cewa ana sa rai abubuwa za su mike a shekarar nan da zarar matatun Dangote da BUA sun fara tace danyen mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel