Sabon hari: 'Yan bindiga 200 sun yi kashe-kashe, sun kora shanu 2000 a Kebbi

Sabon hari: 'Yan bindiga 200 sun yi kashe-kashe, sun kora shanu 2000 a Kebbi

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla 'yan bindiga 200 suka afkawa wasu kauyuka a jihar Kebbi
  • An rahoto cewa, an kashe mutum yayin da aka sace shanu kusan 2000 na mazauna kauyukan a jihar ta Kebbi
  • Ya zuwa yanzu dai jami'an 'yan sanda ba su sanar da komai kan lamarin ba, kuma ba sa daukar waya don jin ta bakinsu

Kebbi - A wani sabon hari da aka kai wasu kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, wasu ‘yan bindiga akalla 200 sun kai hari tare da kashe wasu fararen hula biyar a yayin harin.

A cewar wani ganau Abdullahi Sulaiman, ‘yan bindigar sun kona gidaje tare da kwashe akalla shanu 2000 na mutanen kauyukan da lamarin ya shafa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

An sake kai hari Kebbi, an sace shanu 2000
Sabon hari: 'Yan bindiga 200 sun yi kashe-kashe, sun kora shanu 2000 a Kebbi | Hoto: Channels Tv
Asali: Facebook

Ya kara da cewa akalla kauyuka 12 ne aka kai hari wadanda suka hada da Makera, Tungar taro, Yar danko, Runtuwa, Donka, Nadado, Rijiyar Dutsi, Baure da Tungar Dorawa.

Sai dai a kalla ‘yan bindiga 5 ne sojoji suka kashe yayin da wasu 3 kuma ‘yan banga da suka zo taimakawa sojoji suka dakile yunkurinsu na aikata barna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto cewa, jiragen sama sun kasa ragargazar 'yan bindigan saboda sun fake a kauyukan domin kaucewa ruwan bama-bamai daga jiragen sama, amma komai ya dawo daidai a kauyukan kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kiraye-kirayen da aka yi na wayar salula ga jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar bai kawo haske ba, sannan kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai dawo da sakon da aka aike masa ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga 4, sun cafke wata mata mai safarar makamai

A gefe guda, wakilin Legit Hausa ya tuntubi wani dan asalin Baure da ke zaune a jihar Gombe Musa Muhammadu Baure, wanda ya tabbatar da faruwar hare-haren. Ya ce ya kira gida kuma an shaida masa cewa kanensa ya samu raunuka a yayin da yuake kokarin gudun tsira.

A kalamansa:

"Na kira kanina Adamu, ya shaida min cewa yanzu haka yana kwance , bai kuma san halin da kafarsa ke ciki ba saboda ya taka busasshen itace garin gudu.
"Fatanmu Allah ya kawo karshen wannan barna, amma wallahi muna cutuwa matuka, an ce akwai jami'an tsaro kuma suna kokari, amma dai su kara don Allah."

‘Yan bindiga sun sace wani dan jarida a jihar Abia

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani dan jarida dan asalin Umuahia mai suna Chuks Onuoha, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

An tattaro cewa an yi garkuwa da Onuoha ne a gidansa da ke Ohuhu a karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia.

Onuoha ya kasance tsohon wakilin Abia na Jaridar Sun. An sanar da sace shi ne ga manema labarai ta wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Ohuhu, Enwereuzo Ogbonna ya fitar, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel