Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace wani dan jarida a jihar Abia

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun sace wani dan jarida a jihar Abia

  • Rahoton da muke samu daga jihar Abia na cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da dan jarida
  • Majiya ta ce, dan jaridar da aka kama ya taba aiki da shahararriyar gidan jaridar nan ta Daily Sun a jihar
  • Ya zuwa yanzu, ba a san inda 'yan bindigan suka kai shi, ba a kuma ji labarin batun biyan kudin fansa ba

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani dan jarida dan asalin Umuahia mai suna Chuks Onuoha, The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa an yi garkuwa da Onuoha ne a gidansa da ke Ohuhu a karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia.

Onuoha ya kasance tsohon wakilin Abia na Jaridar Sun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Neja, rayukan mutane sun salwanta

An sanar da sace shi ne ga manema labarai ta wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Ohuhu, Enwereuzo Ogbonna ya fitar, Channels Tv ta ruwaito.

A cewar sa:

“’Yan uwaNSA sun tuntubi kungiyar a safiyar yau don ba da rahoton hakan da misalin karfe 11.00 na dare. A daren jiya ne wasu mutane dauke da makamai su 5 suka shiga gidansa dake Umungasi kusa da Umuagu inda suka yi awon gaba da shi tare da yin awon gaba da motarsa koriyar launikirar Nissan Pathfinder.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"'Yan uwan kuma sun nuna cewa wadanda suka sace shi sun tuntube su da batun kudin fansa."

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

A wani labarin, masu garkuwa da mutane a Zamfara sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 145 domin a sako wadanda suka sace.

Kara karanta wannan

Bauchi: Mummunan Gobara Ta Lakume Shaguna 42 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa

Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa tsagerun sun bukaci a ba su Naira miliyan 5 kowanne mutum a matsayin kudin fansa domin a sako mutanen 29 da aka yi garkuwa da su.

An sace baki sama da 50 da suka dawo daga wani daurin aure a jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar a Dogon Awo, al’ummar da ke tsakanin Tureta da Bakura da ke kan iyakokin jihohin Sokoto da Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel