Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N145m kan bakin bikin Zamfara

  • Mambobin kungiyar masu sayar da wayoyin hannu a Zamfara sun shiga tasku, 'yan bindiga sun yi awon gaba dasu
  • Ya zuwa yanzu, 'yan bindigan sun bayyana bukatar a ba su kudin fansa, suna neman sama da naira miliyan 100
  • Kungiyar dillalan ta yi bayani, ta ce tana ci gaba da tattaunawa da 'yan bindigan don nemo mafita kan lamarin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Masu garkuwa da mutane a Zamfara sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 145 domin a sako wadanda suka sace.

Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa tsagerun sun bukaci a ba su Naira miliyan 5 kowanne mutum a matsayin kudin fansa domin a sako mutanen 29 da aka yi garkuwa da su.

'Yan bindiga na neman miliyoyi kudin fansa a Zamfara
Daga zuwa biki: 'Yan bindiga na neman fansan N1145m kan bakin bikin Zamfara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An sace baki sama da 50 da suka dawo daga wani daurin aure a jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar a Dogon Awo, al’ummar da ke tsakanin Tureta da Bakura da ke kan iyakokin jihohin Sokoto da Zamfara.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Coci, Sunyi Awon Gaba Da Masu Ibada a Ogun

Sai dai kuma sama da 20 daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun tsere yayin da wasu jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin suka kubutar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka sacen an ce dillalan wayoyin hannu ne a dandalin Bebeji Plaza da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara, Premium Times ta ruwaito.

A cewar sakataren kungiyar wadanda abin ya shafa na jihar Zamfara Ashiru Zurmi, ‘yan bindigar sun tuntubi kungiyar ta daya daga cikin wayoyin wadanda lamarin ya rutsa da su, inda suka bukaci naira miliyan 145 a matsayin kudin fansa kafin a sako su.

A cewar Zurmi:

“N145m da aka nema yana nufin naira miliyan 5 ne akan kowanne mutum, amma har yanzu ba mu tattauna ba saboda mun ce ba mu da kudi kuma mu kungiya ce kawai, sai suka ce mu nema a wurin gwamnati.

Kara karanta wannan

Yan Bindigan Da Suka Sace Shugaban CAN a Plateau Sun Bayyana Kudin Da Za A Biya Don Fansarsa

"Mu ne kawai mutanen da ke iya sadawa da 'yan bindigar da wayar daya daga cikin wadanda abin ya shafa."

Zurmi ya yaba da kokarin jami’an tsaro, inda ya ce tun bayan faruwar lamarin, suna kokarin ganin sun ceto ‘yan kungiyar da aka sace.

“Gaskiya su (jami’an tsaro) suna yin iya kokarinsu tun ranar Asabar don ganin sun dawo lafiya.”

Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014

A wani labarin, dakarun runduna ta 26 Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok a shekarar 2014.

Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikici ya barke yayin da aka kashe wani jigon jam'iyyar APC

Hakan na kunshe ne a wani sako da rundunar ya wallafa a shafin Twitter a safiyar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel