Kaduna: 'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga 4, sun cafke wata mata mai safarar makamai

Kaduna: 'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga 4, sun cafke wata mata mai safarar makamai

  • Wani rahoton da muke samu ya bayyana cewa, akalla 'yan ta'adda hudu ne 'yan sanda suka hallaka a jihar Kaduna
  • Wannan na zuwa ne yayin da hare-haren 'yan ta'adda ke kara kamari a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya
  • An ruwaito cewa, an kama wata mata da ake zargin tana da hannu tare da taimakawa 'yan ta'adda wajen aikata barna

Kaduna - Wani rahoton BBC Hausa ya ce, jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun kashe ‘yan bindiga hudu da suka addabi mazauna Saminaka da ke karamar hukumar Lere a jihar.

‘Yan sandan sun kuma kwato bindigu kiran AK47 da Ak49 dauke da alburusai masu da wata motar aiki da ‘yan bindigan ke amfani da su wajen gudanar da munanan ayyukan su.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, jami’an hedkwatar runduna ta musamman dake Abuja (STS) tare da ‘Operation Yaki Kaduna’ sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke barna a kan hanyar Saminaka zuwa Jos.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga 200 sun yi kashe-kashe, sun kora shanu 2000 a Kebbi

An kama wata mata da ake zargin 'yar bindiga ce
Kaduna: 'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga 4, sun cafke wata mata mai taimaka musu | Hoto: Channels Tv
Asali: Twitter

An kama su ne a wata mota kirar Sharon shudiya da wani mai shekara 31 James Dawi daga garin Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato ke tukawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin ‘yan sandan ya kara da bayyana cewa, ‘yan bindigar sun fafata da jami'an tsaro ganin cewa ba za su iya tsallakewa ba, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Sai dai jami’an sun yi nasarar raunata hudu daga cikin ‘yan ta’addan, inda daga baya wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu a wani asibiti da aka kai su.

An ce fafatawar ta dauki kimanin mintuna 30 ne yayin da 'yan sanda suka fi karfin tsagerun.

Hakazalika, rundunar ta ce an kama wata mata da ke rakiya tare da 'yan bindiga, wacce a halin yanzu tana tare dasu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce matar da aka kama yayin gudanar da bincike ta amsa laifin kai makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

A bangare guda, ya ce za a zurfafa bincike domin gano tushen aikata laifin tare da kare dukiyoyi da rayukan al'umma.

Sabon hari: 'Yan bindiga 200 sun yi kashe-kashe, sun kora shanu 2000 a Kebbi

A wani sabon hari da aka kai wasu kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, wasu ‘yan bindiga akalla 200 sun kai hari tare da kashe wasu fararen hula biyar a yayin harin.

A cewar wani ganau Abdullahi Sulaiman, ‘yan bindigar sun kona gidaje tare da kwashe akalla shanu 2000 na mutanen kauyukan da lamarin ya shafa, Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa akalla kauyuka 12 ne aka kai hari wadanda suka hada da Makera, Tungar taro, Yar danko, Runtuwa, Donka, Nadado, Rijiyar Dutsi, Baure da Tungar Dorawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel