Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya

Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya

  • Wani matashi mai suna Anuoluwapo a cikin wasu jerin bidiyo da ya saki, ya nuna yadda ya angwance da wata baturiya a wani kayataccen biki
  • Wani bidiyo da aka fara saki ya nuna yadda ya cika da farin ciki bayan ya tarbi matar a filin jirgin sama yayin da ta iso Najeriya
  • Yan Najeriya da dama sun taya ma’auratan murna, musamman ganin yadda yan uwan Anuoluwapo suka karbi matar hannu bibbiyu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kun tuna matashi Anuoluwapo, wanda ya tarbi masoyiyarsa baturiya a Najeriya? Toh sun yi aure a wani kayataccen biki da aka yi.

Wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok ya nuno su tare a cikin wata mota yayin da ya yi masa take da:

“Barkanmu da shiga rayuwar ma’aurata.”
Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya
Bidiyon yadda matashi ya angwance da amaryarsa baturiya a wani kayataccen biki bayan ta biyo shi Najeriya Hoto: @barrywhiteog215
Asali: UGC

Yan uwansa sun karbeta hannu bibbiyu

Kara karanta wannan

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Wani bidiyon ya kuma nuno su dukka biyun sanye da kayan gargajiya yayin da suka isa gaban mahaifiyar Anuoluwapo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yake a al’adan Yarbawa, wata daga cikin dangin mijin ta zubawa amaryar ruwa a kafa don nuna cewa zamanta a gidan mijinta zai kasance cikin salama kamar yadda ruwa yake sanyaya jiki.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon kasa ya nuna lokacin da aka tarbeta da ruwa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

Isa Thablo ya ce:

“Allah ya albarkaci aurenka dan uwa.”

geesilver ya ce:

“Wannan shine ainahin al’adar Yarbawa…abun takaici mun rasa wannan daraja da dadewa.”

Mammie_phate11 ta ce:

“Ina taya ka murna BarryXchange Allah ya albarkaci gidanka.”

rolandda23 ya ce:

“Kai jama’a wannan ta hadu fa.”

sannisaheed1994 ya ce:

"Allah ya albarkaci gidanka har illa-mashaa- Allah dan uwa.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga

A wani labarin, wasu matan aure a jihar Imo sun yi zanga-zanga a Owerri kan zargin cewa daliban jami’a mata na amfani da ‘shigar nuna tsaraici da manyan mazaunu’ wajen kwace masu mazajensu.

An gano matan auren kimanin su 10 suna tattaki a fadin wajen dakunan dalibai mata, suna gargadin su da su guje ma shigar banza ko kuma su shirya fuskantar hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel