Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

  • Ana tafka muhawara kan abinda ya faru tsakanin wata mata, mijinta, da wani boka a jihar Ogun
  • Bokan ya dirkawa matar aure ciki har ta haihu amma mijinta yace 'dansa ne ba na bokan ba
  • Shi kuwa Bokan ya lashi takobin cewa 'dansa ne kuma ba zai yarda wani kwace masa yaro ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Rikici ya barke tsakanin wani Boka da wani mutumi kan wanene hakikanin Uban 'da a karamar hukumar Owode-Obafemi dake jihar Ogun, Kudu maso yammacin Najeriya.

TheNation ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne a wani gari mai suna Malaka.

Mijin matar mai suna, Sikiru Olaleye yace ya girgiza matuka da ya samu labarin cewa jaririn dake yake tunanin nasa ne ashe na wani Boka mai sune Lamidi Ifaloba.

Yace:

"Ban taba ganin irin haka ba sai a Fim. Ni da uwargidata Sadiya mun samu sabani, sai ta tafi garinsu, Iwo, jihar Osun tare da yaron da ta haifa."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Ƙona Gidaje Sun Raunta Fasto

"Sai na kai ziyara garin don dawo da ita amma abin yaci tura. Har N12,000 na ba iyayenta su bata don tayi kudin motar dawowa gidana, amma ta ki."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Amma sai wasu makwabta suka fara min isgili cewa 'dan dake hannunta ba nawa bane, na wani boka ne."

Sikiru yace bayan shekaru shida basu samu haihuwa ba, matar ta tafi wajen bokan neman magani.

Boka ya dirkawa matar aure ciki
Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Jawabin shi bokan mai suna Ifaloba

Martani kan lamarin, Bokan ya yi bayanin cewa matar ce ta tilasta masa wajen kwanciya da ita ranar da mijinta ya koreta daga gida misalin karfe 1 na dare.

Yace:

"Matar ta zo gida na tace mijinta ya bugeta sakamakon rashin fahimta tsakaninsu."
"Kuma daren akwai sanyi, sai na bata izinin ta kwana zuwa safe yayinda nike wasu ayyuka. Kawai sai tace tana zargin mijinta bai da lafiyar haihuwa shi yasa bata samu haihuwa ba."

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

"Yayinda nike kokarin fita daga cikin dakin, sai ta janyo ni tace in sadu da ita, tana son gwada lafiyarta."
"Daga baya ta dawo tace min ta samu ciki sakamakon jima'in da mukayi kwanaki, sai an fada mata na amince zan karbi yaron."

Jawabin matar, Sadiya Akeem

Matar mai suna Shadiya Hakeem, ya bayyana cewa lallai da gayya tayi jima'i da Bokan a daren saboda ta nunawa mijin cewa shi ke da matsala ba ita ba.

"Ifaloba ne uban yarona, ba Sikiru ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel