Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga

Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga

  • Fusatattun matan aure sun gudanar da zanga-zanga a gaban dakunan kwanan dalibai mata a wata makarantar gaba da sakandare da ke Owerri, jihar Imo
  • Matan auren sun zargi dalibai mata da kwace masu mazaje ta hanyar sanya sutura da ke fito da surar jikinsu
  • Sun kuma kafa dokar cewa daga yanzu duk wacce aka kama da shigar banza, za ta biya tarar N10,000

Imo - Rahotanni sun kawo cewa wasu matan aure a jihar Imo sun yi zanga-zanga a Owerri kan zargin cewa daliban jami’a mata na amfani da ‘shigar nuna tsaraici da manyan mazaunu’ wajen kwace masu mazajensu.

An gano matan auren kimanin su 10 suna tattaki a fadin wajen dakunan dalibai mata, suna gargadin su da su guje ma shigar banza ko kuma su shirya fuskantar hukunci.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga
Yan mata na kwace mana mazajenmu da shigar banza – Matan aure sun yi zanga-zanga Hoto: Newsbreak.ng
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa bata tabbatar da ranar da aka yi zanga-zangar ba, amma mutane sun ce lamarin ya afku ne a ranar Juma’a.

Matan da ke zanga-zanga sun ce duk matan da aka kama sanye da ‘kayan nuna tsaraici’ za su biya tara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Idan kuka karya kowani doka, za ku biya mu N10,000. Idan ya zarce sau daya, za ku rubanya tarar da za ku biya,” cewar wata mata wacce ga dukkan alamu it ace jagorar masu zanga-zangar.

Premium Times ta jiyo cewa dakin kwanan dalibai da matan suka ziyarta a bidiyon da ya shahara ya kasance bangaren ‘Peace Apartment’ a cikin kwalejin tarayya ta Nekede, Owerri.

Daya daga cikin matan da ke zanga-zanga ta yi gargadin cewa:

“Duk wacce ta ki biyan tarar, za ta hadu da mu.”

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Yayin da matar ke magana, wasu mata biyu sun daga kwaleyen sanarwa masu dauke da hotunan irin suturar da suke ganin na nuna tsaraici ne.

Kwalayen na dauke da rubutu kamar haka ‘ba mu yarda da shigar nuna tsaraici ba’.

An jiyo murnar wani namiji yana fadin cewa:

“Yan mata na kwace masu mazajensu. Sun fuskata.
“Duk wadannan yan matan na amfani da shiga ta rashin da’a wajen kwace masu mazajensu. Mata sun fusata. Duk wadannan yan matan basa jin magana.”

Da farko, a lokacin da matan masu zanga-zanga suka shiga dakunan kwanan daliban, wata fusatacciyar daliba ta yi musayar zafafan kalamai da daya daga cikinsu.

Akwai akalla manyan makarantun gaba da sakandare biyar a Owerri, jami’o’I uku, kwaleji biyu, ciki harda jami’ar tarayya da jami’ar jihar Imo.

Ga bidiyon zanga-zangar a kasa:

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Tashin hankali yayin da sojoji ke harba bindigogi a wurin zanga-zangar dalibai

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC sun kama wani mai makarantar koyar da damfarar yanar gizo da dalibansa guda 16.

An kama mutumin mai suna Afolabi Samad tare da dalibansa 16 na makarantar da ke Peace Estate anguwar Lokogoma cikin Abuja kuma ya kama hayar wurin ne a Naira miliyan 3 duk shekara kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter.

Da safiyar Alhamis jami’an ofishin hukumar ta Abuja su ka kama shi bayan samun bayanan sirri akan makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel