Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

  • Dan takarar gwamnan jihar Delta a jam'iyyar APC ya yi hatsari, inda ya samu raunuka da dama a babban birnin tarayya
  • Rahoton da muka samu ya bayyana cewa, dan takarar gwamnan na kan hanyarsa ta zuwa filin jirgi ne lokacin da hatsarin ya faru
  • Hakazalika, motar ta lalace, amma ya bayyana cewa yana samun murmurewa kasancewar bai samu munanan raunuka ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wani dan takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar APC Amb Uba A. Michael ya gamu da mumunan hatsarin mota a hanyar filin jirgin sama da ke kusa da garin Dunamis, Abuja.

An ga shugaban na jam’iyyar APC na Delta yana tuka kansa a nota SUV lokacin da ya yi karo da wata mota a kan hanyar filin jirgin Lube a ranar 14 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al-Mustapha ya yanki tikitin takara kujerar shugaban kasa a 2023

Ko da yake an ga ya tsira da kyar da kananan raunuka, amma an ruwato cewa, motar ta samu mummunan lahani, rahoto PM News.

Dan takarar gwamnan jihar Delta ya yi hatsari
Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya bayyana a sakon wayan salula cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina godiya ga Allah da ya ceci rayuwata, ina cikin koshin lafiya yanzu da kananan raunuka."

Uba Michael shi ne Shugaban UBACLE GROUP kuma ya yi shirye-shirye masu yawa na karfafawa a yankinsa, karamar hukumar Ughelli North aa Jihar Delta, Najeriya.

A yanzu haka yana da burin zama gwamna a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Malama ta tafka hatsari, ta rasu tana hanyar kai wa dalibanta kyautukan ba-zata

Ghasoon Najimi, wata malamar makarantar kasa da firamare wacce ke kan hanyarta ta zuwa makaranta dauke da kyautuka da niyyar ba wa dalibanta bayan sun lashe jarabawar karshen zangon karatu, ta tafka mummunan hatsarin da ya yi sanadin rasa rayuwarta.

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3

An samu labarin yadda hatsarin ya auku a birnin Saudi na Samata sanadiyyar shiga gabanta da wani abun hawa ya yi. Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani sun yi jimamin mutuwar.

Mutane da dama daga birnin sun halarci jana'izar ta. Gwamnan Jazan, Prince Muhammad bin Nasir bin AbdulAziz, ya bayyana alhininsa bisa mutuwar da jajirtacciyar kuma hazikar malamar.

Kafin mutuwarta, Ghasoon Najimi mahaifiya ce ga 'ya'ya hudu da cikin na biyar. Ta so bawa dalibanta kyautar ba-zatar da ta shirya, jaridar Life In Saudi Arabia ta ruwaito.

Karka damu: Shugaba Buhari ya jajantawa tsohon shugaba Jonathan game da mutuwar mukarrabansa

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban Najeriya; Good Ebele Jonathan bisa rashin wasu mukarabbansa biyu a hadarin mota.

Idan baku manta ba, a cikin makon nan ne rahotanni suka karade kafafen watsa labaran Najeriya, inda aka bayyana yadda hadarin mota ya rutsa da tawagar tsohon shugaban kasar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yawancin matukan babur na Okada yan ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas

Jim kadan bayan faruwar hadarin, jiga-jigan 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar suka fara aiko da sako jaje da nuna alhini ga Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel