Shugaban Nijar ya ba Buhari shawarin yadda za a magance matsalar tsaro a Arewa maso yamma

Shugaban Nijar ya ba Buhari shawarin yadda za a magance matsalar tsaro a Arewa maso yamma

  • Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban Jamhuriyar Nijar ya gana shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya
  • Ganawar tasu ta kai ga tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da aikin layin dogon da Najeriya ke yi har cikin Nijar
  • Kana, shugaban na Nijar ya yi tsokaci kan mafita ga matsalar tsaro a Arewacin Najeriya musamman Arewa maso Yamma

FCT, Abuja - Mohammed Bazoum, shugaban Jamhuriyar Nijar, ya ce akwai bukatar kasashen Afirka da ke yaki da ta'addanci su bullo da sabbin dabarun tunkarar kalubalen tsaro a yankunan, The Cable ta ruwaito.

Bazoum ya zanta da manema labarai ne a fadar gwamnatin Najeriya bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Guardian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles

Shawarin shugaban Nijar kan magance tsaro
Shugaban Nijar ya ba Buhari shawarin yadda za a magance matsalar tsaro a Arewa maso yamma | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shugaban na jamhuriyar Nijar ya ce yankin Yammacin Afirka na fama da matsalar tsaro musamman duba da mummunan harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Ya godewa Buhari bisa goyon bayan da yake baiwa kungiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), yana mai cewa zuba kudi da Najeriya ta yi ya sa aikin ya cimma gashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa wani abin tsari ne da kasashen da ke fuskantar kalubale iri daya na tsaro suka bullo da shi kuma muna son kawo irin wannan tsari a kasashen Sahel, Mali, Nijar, Burkina Faso da dai sauransu.
"Saboda wannan tsarin ya ba mu damar magance wata barazana ta bai daya a yankin tafkin Chadi kuma mun gamsu da lamarin saboda ya ba mu damar shawo kan lamarin kuma muna son yin irin wannan a kasashenmu.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

“Dole kuma in yaba wa kokarin gwamnan jihar Zamfara. Har ila yau, abin da ya faru kwanan nan a Kaduna ya nuna cewa ana samun karuwar barazanar da muke fuskanta wanda hakan ke nufin sai mun tsara wata sabuwar hanya don mu iya magance wannan barazana."

Mun gode da aikin layin dogo, shugaban Nijar ga Buhari

Bazoum ya ce ya tattauna da shugaban kasa kan aikin layin dogo na Kano-Katsina-Maradi da kuma amfanin da zai samar ga kasashen biyu.

A cewarsa:

“Na zo nan ne domin in gode wa Shugaba Buhari bisa kokarinsa na ganin an fara gudanar da wannan aiki, kuma ina fatan zai dore saboda wannan aikin zai canza mu’amalar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
"Mun kuma yi magana game da bututun iskar gas ganin cewa gas da mai a yanzu sun zama batu na siyasar duniya, na tattalin arzikin duniya."

Malaman Qadiriyya da wasu kungiyoyi sun gana da Osinbajo, sun ce masoyin 'yan Najeriya ne

Kara karanta wannan

Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

A wani labarin, wasu limamai, malaman addinin Islama, da shugabannin matasa a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris sun ziyarci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake Abuja.

Da yake karbar bakuncinsu, Osinbajo ya bayyana cewa hadin kai da hakuri sune muhimman dabi’un da ake bukata domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin al'umma mai addinai daban-daban kamar Najeriya.

Tawagar malaman da shuwagabannin kungiyoyi sama da 25 sun fito ne daga manyan cibiyoyin addini; majalisar malamai ta kasa, kungiyar Qadiriyya, Fitiyanul Islam ta Najeriya, Darikar Dariya, da majalisar matasan musulmi ta kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel