Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

  • Ministan yada labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta taka rawar gani a fannin tsaro
  • Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen tabbatar da tsaro da aminci ta hanyar inganta sufurin jiragen kasa
  • Kalaman Lai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare a sassan kasar, ciki har da harin da aka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a watan Oktoban 2021

Abuja - Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce gwamnatin Buhari ta taka rawar gani matuka wajen samar da ababen more rayuwa ga 'yan Najeriya.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taron manema labarai a Abuja, TheCable ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi kokari matuka wajen tabbatar da tsaro ta hanyar inganta sufurin jiragen kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ba Najeriya kadai ke fama da tsadar kayan abinci da man fetur ba

Muna alfahari da yadda 'yan Najeriya ke more jirgin kasa
Muna alfahari: Kalaman Lai Mohammed kan yadda 'yan Najeriya ke jin dadin jirgin kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna alfahari da cewa a mulkinmu, 'yan Najeriya sun sake samun damar tafiya ta jirgin kasa, a wannan karon cikin dadin rai da kwanciyar hankali."
“Legas-Ibadan, Abuja-Kaduna, Warri-Itakpe-Ajaokuta da layin dogon zamani na Abuja sune misalan jan aikin mu a fannin jirgin kasa.
"Kuma yanzu muka fara. Muna da aikin gyaran layin dogo na Gabashin Fatakwal-Maiduguri wanda ya ratsa ta Ribas, Imo, Anambra, Benue, Enugu, Ebonyi, Gombe, Yobe, Adamawa da Borno, da kuma tashar jirgin kasa ta Bonny Deep Sea.
"Muna da layin layin dogon Kano-Maradi wanda ya ratsa ta wasu cibiyoyin tattalin arzikin kasar nan da suka hada da Kazaure, Daura, Katsina har zuwa garin Jibiya da ke kan iyaka da birnin Maradi a Jamhuriyar Nijar."

Kalaman Lai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare a sassan kasar, ciki har da harin da wanda aka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a watan Oktoban 2021.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Neja, sun sace mutane sama da 40

A farkon watan Maris, wani jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya a tsakiyar hanya bayan da aka ce man sa ya kare a tsakiyar daji.

Gwamnati ta yi kokari wajen inganta tsaro

Da yake karin haske a taron manema labarai, ministan ya ce kasar na kara samun zaman lafiya tare da samun nasarori a yakin da ake da ‘yan tada kayar baya da kuma ‘yan fashi.

Ya kara da cewa:

“Ina alfahari da jami’an tsaron mu, maza da matan mu da ke sanye da kaki. Duk da dimbin kalubalen tsaro, suna rayuwa daidai da tsari. Nasarorin da aka samu a baya-bayan nan a yakin da ake da Boko Haram da ISWAP na kara karfin gwiwa.
“A yayin da ake lalata matsugunan ‘yan ta’adda da sansanoninsu, dubunnan ‘yan ta’adda da iyalansu suna ta mika wuya cikin dandazo.
“Aikin jami’an tsaron ya samu ne bisa jagorancin da shugaba Buhari ya bayar da kuma jajircewar rundunar sojin kasar da shugabanninta."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tashin hankali yayin da tankar gas ta fashe a kusa da wani banki

Harin jirgin Abuja-Kaduna: Mun garzaya da wadanda suka jikkata asibiti: Gwamnatin Kaduna

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana halin da ake ciki game da harin Bam din da aka kaiwa layin dogon Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin, 28 ga watan Maris, 2022.

Kwamishanan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa jami'an Sojoji sun dira wajen kuma suna tsare fasinjojin.

A cewarsa, an kwashe fasinjojin daga cikin dajin zuwa ckin gari yayinda aka garzaya da wadanda suka jikkata asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel