Karin bayani: Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles

Karin bayani: Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles

  • Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta kori masu horar da 'yan wasan Super Eagles
  • Hukumar kwallon kafan Najeriya (NFF) ta bayyana dakatar dasu ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau dinnan
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da kasar Ghana ta haramtawa Najeriya zuwa gasar na cin kofin duniya a Qatar

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), ta kori Augustine Eguavoen daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan ya biyo bayan gazawar da Super Eagles ta Najeriya ta yi na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2022, bayan da suka tashi kunnen doki da Black Stars ta kasar Ghana a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

An dakatar da masu horar da 'yan wasan Super Eagles
Yanzu-Yanzu: Bayan rasa damar shiga gasar kofin duniya, Najeriya ta fatattaki kocin Super Eagles | Hoto: independent.ng
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Daraktan yada labarai na NFF, Ademola Olajire, ya ce a halin yanzu NFF ta janye kwantiragin shekaru biyu da rabi da ta yi da daukacin ma’aikatan fasaha na hukumar ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda Blueprint ta tattaro.

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Za a sanar da sabbin ma'aikatan bayan an yi nazari mai kyau don jagorantar sabon aikin karfafa wa Super Eagles don fuskantar kalubale nan gaba yadda ya kamata."
"Muna godiya ga masu horar da 'yan wasa da jami'an kungiyar bisa hidimar da suke yi wa kasa kuma muna yi musu fatan samun nasara a harkokinsu na gaba."

Matasa sun fara lalata filin kwallon Abuja sakamakon kashin da Najeriya ta sha hannun Ghana

A wani labarin, wasu matasa yan Najeriya da suka je kallon kwallon Najeriya da Ghana a filin kwallon Moshood Abiola dake birnin tarayya Abuja sun fusata, sun haukace.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

Wani dan jaridan Ghana, Yaw, ya dauki bidiyon matasa da yammacin nan sun bazu cikin filin kwallon bayan waje da Najeriya da kasar Ghana tayi kuma ta hanata zuwa gasar kwallon duniya a Qatar bana.

Bidiyon ya nuna jami'an tsaron sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa matasan amma da alamun abun ya yi kamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel