Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

  • 'Yan takarar shugaban kasa, da sanata a Najeriya sun yi martani kan mummunan harin 'yan bindiga a jirgin kasan Kaduna
  • Jiga-jigan 'yan siyasa sun hada da Atiku Abubakar, Bukola Saraki da tsohon Sanata Shehu Sani daga Kaduna
  • Sun yi Allah wadai da harin, sun kuma yi tsokaci tare da bayyana neman mafita daga gwamnatin Najeriya

'Yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki da tsohon dan sanata, Shehu Sani sun yi Allah wadai da harin 'yan ta'adda a kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya afku da yammacin jiya Litinin 28 ga watan Maris.

‘Yan siyasar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara maida hankali wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

Harin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna: Atiku, Saraki, Sani Shehu, sun yi Allah wadai da harin
Harin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna: Atiku, Saraki, Sani Shehu, sun yi Allah wadai da harin 'yan bindiga a Kaduna | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

A wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce:

Kara karanta wannan

Hasashen Shehu Sani: Abubuwan da Abba Kyari zai yi gamo dasu a magarkamar Kuje

"Harin da aka kai a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda aka ruwaito ya yi sanadin jikkatar mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu abin Allah wadai ne. Ya kamata gwamnati ta dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matsayin babban lamari. Ina jaje da addu'a ga duk wanda abin ya shafa."

A bangare guda, tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Muna bukatar mafita ta hakika don magance wannan barazana da kuma kawo karshen asarar rayukan ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba. Ina addu'a ga daruruwan mutane da iyalansu da wannan harin na rashin hankali ya shafa.
"Ina addu’ar a kama maharan nan take, kuma jami’an tsaronmu su kara himma a kan dukkan hanyoyinmu, tashoshin jiragen ruwa, da na jiragen kasa.”

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

Hakazalika, tsohon dan sanata daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya koka da cewa ba a koyi darasi daga harin da aka kai a baya ba kuma an yi watsi da alkawuran da aka yi a wancan lokacin.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Sun kashe wasu, sun raunata wasu, wasu kuma sun yi garkuwa da su. Harine da za a iya hana faruwarsa. Ba a koyi darussa daga bala'in baya ba. Jiragen kasan ba su da na'urorin gano abubuwan zargi da za su gano abubuwan fashewa kuma an yi watsi da alkawarin amfani da jirage masu saukar ungulu don kare jiragen kasa."

Harin jirgin Abuja-Kaduna: Mun garzaya da wadanda suka jikkata asibiti: Gwamnatin Kaduna

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana halin da ake ciki game da harin Bam din da aka kaiwa layin dogon Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin, 28 ga watan Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

Kwamishanan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa jami'an Sojoji sun dira wajen kuma suna tsare fasinjojin.

A cewarsa, an kwashe fasinjojin daga cikin dajin zuwa ckin gari yayinda aka garzaya da wadanda suka jikkata asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel