Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

  • Gwamnatin tarayya ta nemi yan Najeriya da su tallafa da kudin magungunan marasa lafiyan da harin jirgin kasan Kaduna ya ritsa da su
  • Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce hukumar sojin kasa ta baiwa marasa lafiyan kulawa a asibitinta ba tare da ta karbi ko kwabo ba
  • Sai dai ya ce wasu daga cikin marasa lafiyan na bukatar magunguna wadanda ba a kasar nan ake yin su ba, don haka yan Najeriya su kawo gudunmawa

Kaduna - Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya bukaci yan Najeriya da su kawo gudunmawar kudi domin kula da wadanda harin jirgin kasa na ranar Litinin ya ritsa da su.

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da yan bindiga suka far ma jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Harin jirgin kasa: FG ta bukaci yan Najeriya da su hada kudi don yiwa marasa lafiya magani
Harin jirgin kasa: FG ta bukaci yan Najeriya da su hada kudi don yiwa marasa lafiya magani Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Amaechi, wanda ya ziyarci wajen harin a ranar Talata, ya ce ba don an toshe sayan manyan kamarori da na’urori na layin dogo da kudinsu ya kai naira biliyan 3 ba, da an dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce kayan zai kawar da duk wani bakin wuri a kan hanyoyin jiragen kasa a fadin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a lokacin da ya ziyarci wadanda abun ya ritsa da su wadanda ke samun kulawa a asibitin rundunar sojin Najeiya na 44 a Kaduna a ranar Laraba, Amaechi, ya ce rundar sojin ta basu kulawa ba tare da karbar ko sisin kwabo ba.

Sai dai kuma, ya ce wasu marasa lafiyan na bukatar magunguna da ba a yinsu a kasar, inda ya bukaci yan Najeriya da su taimaka wajen tattara kudin, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Amaechi ya ce:

“Muna ta tattaunawa tare da babban daraktan lafiyan, rundunar sojin bata karbi ko sisin kwabo ba kan kowani mara lafiya. Sun bayar da isasshen kulawar da za su iya ba kowani mara lafiya.
“Kun ga marasa lafiyan da ke da kuna da kuma wata da ke da harbin bindiga a zuciyarta, za a kawo wani kwararre a gode kan wannan don ganin ko za a yi aiki ko ba za a yi ba don cire alburushin.
“Sun ce suna da marasa lafiya bakwai ne da suka rage sannan an sallami sauran. Ma’aikatar, da gwamnatin tarayya sun yaba da rundunar soji kan wannan aiki da ta yi. Amma abu daya da na fada ma yan Najeriya shine su hada kai da hukumar asibitin sannan mu ga nawa za su bayar da gudunmawa domin warkar da marasa lafiyan.
“Tabbas wadannan magungunan ba a nan ake yin su ba, kwararrun da suke kawowa daga waje ba sa aiki da sojoji, don haka dole ne su biya su. Za mu yi iya kokarinmu don ganin irin gudunmawar da za mu iya bayarwa ga mahukuntan asibitin don taimakawa wajen kula da marasa lafiyan.”

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

A gefe guda, mun ji cewa Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar, ta bayyana cewa bayanan sirri sun nunawa hukuma cewa ‘yan ta’adda su na shirin kai wannan mummunan hari.

Wani babban jami’in tsaro ya shaidawa manema labaran cewa da an ga dama, da an hana hakan faruwa.

Bayan nan, gwamnatin Kaduna da babbar rundunar sojoji da ke jihar ta rubutawa hukumar NRC takarda, ta na neman dakatar da tafiyar dare saboda irin haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel