Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

  • Ministan sufuri na tarayya ya ziyarci inda ‘yan ta’adda su ka tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja
  • Hon. Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro
  • A karshe rashin kayan aikin ya jawo an tafka asarar dukiya, sannan an rasa Bayin Allah da-dama

Abuja - A ranar Talata, 29 ga watan Maris 2022, Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasa.

Daily Trust ta rahoto Hon. Rotimi Amaechi ya na mai cewa sai da ya bukaci a kawo kayan aikin tsaro na zamani domin a magance aukuwar wannan ta’adin.

Amaechi wanda ya yi magana da manema labarai yayin da ran shi yake a bace, ya ce gwamnati za ta iya magance abin da ya wakana a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A cewar babban Ministan sufurin kasar, da a ce wasu ba su hana a fitar da Naira biliyan 3 wajen sayen na’urori da kayan aiki ba, da duk wannan ba ta faru ba.

Ministan ya ce kayan aikin za su taimaka wajen tsare jirgin kasan a duk wasu wurare masu hadari.

Mutane 8 sun mutu a cikin 970

Vanguard ta ce Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ziyarci inda abin ya faru, ya kuma tabbatar da mutane takwas sun mutu, sannan 25 su na jinya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jirgi
Jirgin kasan Legas - Ibadan Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Mutane 398 ne suke cikin jirgin a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari, ba 970 da ake fada ba.

“Mun san yadda matsalolin za su kasance idan sun auku. Mun san mu na bukatar kayan tsaro na zamani a kan hanya, mun bukaci a kawo mana su.”

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

“Bari in tsaya a nan saboda gudun batawa mutane da yawa rai. Amma na ji shugaban kasa ya bada umarnin cewa dole a kawo kayan aikin nan da wuri.”
“Da a ce mu na da wadannan kayan aiki a kan dogo, za a iya ganin duk abin da ke kan hanya. Mun yi gargadi cewa za a rasa rayuwa, yanzu an yi asara.”
“Ba mu san mutane nawa aka dauke ba, kuma gaba daya kudin kayan aikin nan bai wuce N3bn ba. Yanzu mun yi asarar jirgi, dogo, da kuma mutane.”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya ce a lokacin da ya fara neman a kawo wadannan kayan aiki, Dalar Amurka ba ta wuce N400, yanzu ta kai N500, ya ce wasu ne su ke kawo masa cikas.

Wadanda abin ya rutsa da su

Ku na da labari cewa 'yan bindiga sun harbi Kwamishinan lafiya na jihar Katsina watau Dr. Yakubu Nuhu Danja da aka tare jirgin ƙasa a hanyar zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Sannan an nemi tsohon 'dan takarar 'dan majalisa a Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi babu labarinsa. 'Yan bindigan sun kuma harbi Ibrahim Wakala a jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel