Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

  • Akwai bayanan sirri da suka nunawa hukuma yiwuwar kai wa jirgin kasan Kaduna-Abuja hari
  • Amma jami’an tsaro ba su dauki matakin da ya kamata ba, har ‘yan ta’adda suka yi mugun ta'adi
  • Hukumar NRC ta ki daukar shawarwarin gwamnati da sojoji na cewa a daina yin tafiya cikin dare

Kaduna - A daren Litinin ne ‘yan ta’adda suka tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da ya dauko mutane kusan 300. A sanadiyyar haka aka yi asarar rayuka.

Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar, ta bayyana cewa bayanan sirri sun nunawa hukuma cewa ‘yan ta’adda su na shirin kai wannan mummunan hari.

Wani babban jami’in tsaro ya shaidawa manema labaran cewa da an ga dama, da an hana hakan faruwa.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Sunaye da lambar wayoyin mutum 398 da suka sayi tikirin jirgin Abuja zuwa Abuja

Bayan nan, gwamnatin Kaduna da babbar rundunar sojoji da ke jihar ta rubutawa hukumar NRC takarda, ta na neman dakatar da tafiyar dare saboda irin haka.

Shugaban NRC mai kula da harkar jirgin kasa, Injiniya Fidet Okhiria ya samu wannan wasiku, amma duk da haka ya ki karbar shawarar da aka kawo masa.

Okhiria ya ce tun Disamban 2021 aka ja-kunnensu, amma aka cigaba da jigilar fasinjoji cikin dare domin daina aiki ya na nufin ‘yan ta’adda sun yi nasara kenan.

Jirgin kasa
Jirgin kasan Kaduna-Abuja Hoto: technext.ng
Asali: UGC

Mutanen Turji sun shigo Kaduna

Jaridar ta ce kwanaki aka samu labari yaran Turji sun shigo jejin Buruku da ke garin Chikun, kuma sun fara kafa sansani a Falalin Dutse da Rafin Dawa Danne.

Wadannan miyagun ‘yan bindiga sun zo Kaduna ne bayan wani gawurtaccen mai satar mutane da ake kira Kwalba ya gayyace su domin su tare jirgin Kaduna-Abuja.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Baya ga tashar jirgin kasa da ke Rigasa, ‘yan bindigan sun ci burin shiga makarantar NDA ta sojoji.

Amma mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ya ce ba su da labarin wani bayanin sirri da ya yi nuni ga cewa za a kai wa jirgin kasan hari.

'Yan bindiga sun tare a jeji

Haka zalika a watan na Maris, an samu labari ‘yan bindiga dauke da babura kusan 300 sun bar yankin Danjibga a Zamfara, sun shiga Rijana ta cikin dajin Birnin Gwari.

A karshe duk ba a dauki mataki ba har aka dasa bam a hanyar jirgin. Hakan ya sa wasu su ke ganin cewa ‘Yan Boko Haram sun taimaka wajen yin wannan ta’adi.

Mun san za ayi haka - Minista

Ministan sufuri na tarayya, Hon. Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe kudi wajen sayan wasu kayan tsaro na zamani domin gudun hakan ta faru.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Amaechi ya koka da cewa a karshe rashin kayan aikin ya jawo an tafka asarar dukiya, sannan an rasa Bayin Allah da-dama saboda kyashin a fitar da Naira biliyan uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng