Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

  • A karshe Shugaba Buhari ya yi martani kan harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Kaduna
  • Buhari ya ce ya kadu matuka da samun labarin wanda irinsa na biyu kenan da ya faru a baya-bayan nan
  • Shugaban kasar ya kuma yi jaje ga yan uwan wadanda suka rasa ransu a harin yayin da ya yi addu'an samun lafiya ga wadanda suka jikkata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki kan harin da yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwa da raunata mutane da dama a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

A ranar Talata, 29 ga watan Maris, shugaban kasar ya ce harin ya yi masa ciwo sosai, wanda shine na biyu da aka kai a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Buhari ya yi Allah-wadai da tayar da jirgin kasan fasinjojin, inda ya bayyana shi a matsayin abun damuwa matuka, Daily Trust ta rahoto.

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari
Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa daga kakainsa, Mallam Garba Shehu, shugaban kasar ya ce:

“Kamar yawancin yan Najeriya, faruwar lamarin ya yi mani ciwo sosai, shine irinsa na biyu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji da ba a san adadinsu ba sannan wasu sun jikkata.
“Harin kan jirgin kasan, wanda yake shine hanyar sufuri mafi tsira ga mutane da dama abin takaici ne; kuma zukatanmu na tare da iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka jikkata addu’a.”

Buhari ya yi umurnin gaggauta kammala duk dukkan tsare-tsare don aiwatar da zuba tsaro da sa ido kan hanyoyin jiragen kasa na Abuja-Kaduna da Lagas-Ibadan.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

Ya kuma umurci hukumar kula da harkokin jiragen kasan Najeriya da ta gaggauta gyara layukan dogo da suka lalace sannan su koma bakin aikinsu na yau da kullun ba tare da jinkiri ba, rahoton Nigerian Tribune.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Shugaban kasar ya bayar da wadannan umurnin ne a Abuja, a ranar Talata, bayan samun jawabai daga shugabannin tsaro karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, tare da shugaban hafsan soji, Lt-General Faruk Yahaya, shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Isiaka Amao, sufeto janar na yan sanda, Usman Baba da kuma Manjo Janar Samuel Adebayo, shugaban hukumar leken asiri da darakta janar na hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi a fadar shugaban kasa."

Shugaban kasar ya kuma bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su dawo da dukkan fasinjojin da aka sace tare da tabbatar da ganin cewa an bi sahun ‘yan ta’addan sannan su fuskanci shari’a.

Ya jadadda umurnin da ya baiwa sojoji a baya na su yi maganin yan ta’adda ba tare da jin kai ba sannan ya nemi su hukunta duk wanda ke kera bindigar AK-47 ba bisa doka ba.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya ziyarci Kaduna

A gefe guda, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya isa jihar Kaduna, yan sa’o’i kadan bayan harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasa da ke dauke da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya ce ubangidan nasa na a hanyarsa ta zuwa Lagas domin halartan taron ‘birthday’ din Tinubu amma sai ya karkata akalar tafiyar tasa zuwa Kaduna bayan ya samu labarin irin barnar da harin ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel