Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

  • Bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, rundunar sojin Najeriya ta bayyana abin da ta fada wa shugaban
  • Lucky Irabor, babban hafsun tsaron Najeriya ne ya tattauna da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da Buhari
  • Ya bayyana adadin mutanen da aka kashe tare da bayyana adadin wadanda suka jikkata kana da yunkurin soja na kawo mafita

Abuja - Lucky Irabor, babban hafsan tsaron kasar nan, ya ce mutane bakwai ne suka mutu, yayin da wasu mutum 29 suka samu raunuka a harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin kasa a ranar Litinin.

Jirgin dai wanda ya taso daga Abuja, tuni yana Kaduna amma bai isa tasharsa ba lokacin da aka kai masa hari, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Sojojin Najeriya sun gana da Shugaba Buhari
Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Irabor ya ce jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da lamarin ya faru.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun zo ne domin mu yi wa shugaban kasa bayani kan abu mara dadi na jiya, inda wasu ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga suka tayar da bam a kan titin jirgin kasa, sannan suka lalata jirgin na fasinja.
“An kashe ‘yan Najeriya bakwai, wasu 29 sun jikkata, wasu kuma an yi garkuwa da su, kuma har yanzu ba mu kai ga tantance adadinsu ba.
“Mun je wurin da abin ya faru a safiyar yau, mun duba yankin gaba daya sannan muka ba da umarni kan abin da za a yi kuma mun zo ne domin mu yi wa shugaban kasa bayani kan wannan ci gaba.”

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

Babban hafsan tsaron ya kara da cewa hukumomin tsaro za su kara kaimi domin hana sake afkuwar harin na ranar Litinin, kamar yadda Pulse ta tattaro.

Ya kara da cewa:

“Kalubalen rashin tsaro dawwamammen lamari ne don haka akwai bukatar jami’an tsaro su kasance a cikin shiri 24/7. Wannan abin takaici ne kuma mun yi imanin cewa darussan da ke cikin wannan lamari su ne abin da ya kamata mu gina kan ci gaba.
“Watakila zan iya amfani da wannan dama kuma in tabbatar wa al’ummar kasar cewa bisa ga umarnin shugaban kasa, za mu dauki dukkan matakan da suka dace, ba wai kawai mu kama wadanda ke da hannu a wannan mummunar aika-aika ba, za su fuskanci fushin doka.
"A nan gaba, tabbas, za a sami karin tsaro ga al'umma kuma ina so in yi kira ga kowa da kowa ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum."

Kara karanta wannan

Abokan Twitter: Likita ta mutu bayan abokai sun karyata hari ya rutsa da ita a Kaduna

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

'Yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki da tsohon dan sanata, Shehu Sani sun yi Allah wadai da harin 'yan ta'adda a kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya afku da yammacin jiya Litinin 28 ga watan Maris.

‘Yan siyasar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara maida hankali wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

A wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce:

"Harin da aka kai a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda aka ruwaito ya yi sanadin jikkatar mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu abin Allah wadai ne. Ya kamata gwamnati ta dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matsayin babban lamari. Ina jaje da addu'a ga duk wanda abin ya shafa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel