Abokan Twitter: Likita ta mutu bayan abokai sun karyata hari ya rutsa da ita a Kaduna

Abokan Twitter: Likita ta mutu bayan abokai sun karyata hari ya rutsa da ita a Kaduna

  • A ranar Litinin 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan layin dogon Abuja zuwa Kaduna kuma hukumomin Najeriya sun tabbatar mummuna
  • Wannan hari ya bar dangin wata likita da abokan arziki cikin zulumi yayin da aka gano ta mutu a mummunan harin
  • Kafin rasuwar Dr. Chinelo Nwando Megafu ta rubuta wani sako a shafin Twitter game da harin, inda tace an harbe ta a kafa, amma jama'a suka tozartata a yanar gizo

Chinelo Nwando Megafu, likitar hakora, ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a wani mummunan harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a daren ranar Litinin, 28 ga watan Maris, inji rahoton The Cable.

Tun da farko dai jirgin na kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna ne wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari a unguwar Kateri-Rijana da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Likitar da ta mutu a harin 'yan bindiga
Abokan Twitter: Likita ta mutu bayan abokai sun karyata hari ya rutsa da ita a Kaduna | Hoto: @PreciousSegun
Asali: Facebook

An ce ‘yan bindigar sun tarwatsa titin jirgin ne da abin fashewa bayan sun kai farmaki kan fasinjojin da ke cikinsa.

Jim kadan bayan kai harin, Chinelo ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an harbe ta a cikin jirgin kasa yayin da take neman addu'o'i daga mabiyanta.

Sai dai, neman addu'o'i a Twitter ya haifar da martani daban-daban yayin da wasu ke nuna tausayin ta, wasu kuwa suka bayyana ta batun ta a matsayin zunzurutun karya.

Martani 'yan Najeriya game da rubutunta na neman addu'o'i

Jama'a a shafin Twitter sun kuma ce ba za ta iya rubutu a shafin na Twitter da gaske ta samu raunukan harbin bindiga a harin.

A ranar Talata, 29 ga watan Maris, kwatsam shafin Twitter ya cika da rubuce-rubucen da ke cewa likitar ta mutu sakamakon harbin bindiga da ta samu a harin.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

Daya daga cikin abokan aikin Chinelo ne ya ba da labarin mutuwar wannar likitar sakamakon mummunan harin.

Baya ga Azman, kamfanin jirgin Air Peace ya dakatar da aiki a Kaduna

A wani labarin, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kamfanin jiragen sama na Air Peace ya dakatar da ayyukansa zuwa filin jirgin sama na Kaduna.

Wata majiya ta alakanta faruwar lamarin ga harin da aka kai a kusa da filin jirgin Kaduna a karshen makon jiya.

Idan baku manta ba, an ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka bindige wani mai gadi da ke aiki a hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel