Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

Harin jirgin kasan Kaduna: Halin da dangin wadanda ke cikin jirgin ke ciki a yanzu

  • Iyalai da dama sun shiga tashin hankali yayin da suke son jin halin da danginsu ke ciki bayan harin jirgin Kaduna
  • Wannan na zuwa ne tun bayan da rahotanni suka bayyana an kai hari kan wani jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna
  • Lamarin bai yi dadi ba, domin akalla mutane 16 sun mutu inji wani rahoto da gwamnatin Kaduna ta fitar a yau

Wasu iyalan fasinjojin da ke cikin jirgin kasan da ya nufi Kaduna da aka kai wa hari a ranar Litinin sun ce har yanzu ba su san halin da ‘yan uwansu ke ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Da suke magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a tashar jirgin kasa ta Rigasa da ke Kaduna ranar Talata, sun ce har yanzu ba su ji daga gare su ba, sa’o’i 14 da faruwar wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: An fara gano yawan mutanen da suka mutu a harin jirgin ƙasan Kaduna

Dangi na cikin firgici
Harin Jirgin Kasa: 'Yan uwa suna fargabar inda danginsu suka shiga | Hoto: tvcnews.ng
Asali: UGC

Don haka sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta kawo musu dauki domin rage kawar musu fargabar da suke ciki.

Bamu san halin da 'yan uwanmu ke ciki ba

Mista Mohammed Barau, mazaunin unguwar Ungwan Rimi da ke Kaduna, ya ce ya je tashar jirgin ne domin samun cikakken bayani kan lamarin, inda ya ce kanin sa na cikin jirgin da aka kai wa harin.

A cewarsa:

“Mun kira layinsa sau da yawa amma bai amsa ba, sai daga baya abokinsa da ya zauna kusa dashi a cikin jirgin ya dauka ya gaya mana cewa dan uwana ya ajiye wayarsa a kan kujera kuma bai san inda yake ba.
“Lokacin da muka sake kokarin sake kira, wayar a kashe, kuma da muka kira abokin, shi ma ba ya dauka.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa: An gano gawarwakin mutane da yawa a wurin da 'yan bindiga suka kai hari, Gwamnatin Kaduna

“A yanzu ya kamata gwamnati ta fitar da cikakken jerin mutanen da aka kashe, wadanda suka jikkata, da kuma adadin mutanen da aka kwashe.
"Akalla, idan aka yi haka, zai ba mu kwanciyar hankali, amma har yanzu ba mu ji komai ba."

Haka kuma, Miss Lami Gombo, wata mazauniyar Kudenden a Kaduna, ta ce har yanzu ba a ji ta bakin dan uwanta da ke cikin jirgin ba.

“Layukan wayarsa a kashe suke; mun je Asibitin Sojojin Najeriya, amma ba mu gan shi a can ba.
“Lamarin abin damuwa ne; dukkan iyalai na rude ko dan’ wanmu yana raye, ya mutu, ko kuma an yi garkuwa da shi."

Wasu da suka zanta da NAN sun bayyana irin wannan yanayi, inda suka kara da cewa hankalinsu a tashe yake sakamakon rashin sanin halin da ‘yan uwansu ke ciki.

Wani ma’aikacin hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, wanda shi ma yana cikin jirgin kasan, ya shaida wa NAN cewa wasu daga cikin fasinjojin sun gudu cikin daji domin tsira a lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Wani mazaunanin Zariya ta jihar Kaduna, Usman Aliyu Makwa, ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa, ya zuwa yanzu dai bai samu jin ta bakin wansa da yake fargabar jirgin ya shigo daga Abuja zuwa Abuja.

"Ya kira gida da rana cewa, zai dawo Zariya a jiya, amma bai shigo ba kuma bai kira waya ba. Hakanan, matarsa ta kira shuru wayar ba ta shiga wannan yasa ta kira take fadamin bata ji daga gare shi ba. Allah ne masani, ni dai yanzu haka ina can, bansan ya zanyi ba."

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

A wani labarin, 'yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bukola Saraki da tsohon dan sanata, Shehu Sani sun yi Allah wadai da harin 'yan ta'adda a kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wanda ya afku da yammacin jiya Litinin 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja

‘Yan siyasar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara maida hankali wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasar.

A wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na Twitter, ya ce:

"Harin da aka kai a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda aka ruwaito ya yi sanadin jikkatar mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu abin Allah wadai ne. Ya kamata gwamnati ta dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matsayin babban lamari. Ina jaje da addu'a ga duk wanda abin ya shafa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel