Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

  • Tsagerun yan bindiga sun bude wuta a kan motar wasu matafiya a hanyar Yan Tumaki – Danmusa da ke jihar Katsina
  • Lamarin wanda ya afku a ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji biyar tare da jikkata wasu uku
  • An tattaro cewa hakan na iya zama ramuwar gayya sakamakon matsawa yan fashin daji da jami'an tsaro suka yi a yankin

Katsina - Premium Times ta rahoto cewa an kashe fasinjoji biyar sannan wasu uku sun ji munanan rauni bayan yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota a hanyar Yan Tumaki – Danmusa da ke jihar Katsina, a safiyar Asabar.

Karamar hukumar Danmusa na daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Katsina, inda ta raba iyaka da dajin Rugu da yankuna irin su Safana, Kankara da garuruwan jihar Zamfara inda 'yan fashi ke yin barna sosai.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5
Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani shaida, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Musa, ya shaidawa Premium Times cewa yawancin fasinjojin sun fito ne daga Benin a jihar Edo yayin da daya yake dawowa daga birnin tarayya Abuja inda ya je kai odar kaji.

Ya ce fasinjojin yan asalin Gobirawa da Kaigar Malamai da ke jihar Katsina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Motar, kirar Golf, ta bar Yantumaki zuwa garin Danmusa da safiyar. Fasinjojin sun kwana a Yantumaki saboda isowar dare suka yi. Da safe, sai suka dauki mota zuwa garin Danmusa inda daga nan za su hau babura zuwa kauyukansu.
“Amma sai aka farma motar yan mintuna kadan bayan sun bar Yantumaki. Abun da ya faru shine cewa yan bindiga sun hango motar sannan suka yi kokarin tsayar da ita amma direban ya ki tsayawa, hakan ya sa yan bindagar suka bude masu wuta. Motar ta yi yar dungure sannan ta daki wata bishiya.”

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

Mista Musa ya ce yan bindigar sun tsere a lokacin da hatsarin ya afku.

Musa ya kara da cewa:

“Wasu bayin Allah ne suka sanar da yan sanda a Danmusa sannan suka kwashi gawarwakin da kuma kai mutane uku da suka jikkata asibiti. Tuni muka birne mamatan yayin da sauran uku ke samun kulawa a asibiti.”

Dalilin kai harin

Wata majiya da ke zama a yankin wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigar na kai hare-hare ne domin yin ramuwar gayya kan barin wuta da jami’an tsaro ke yi masu.

“Hatta da kisan fasinjojin an ce ‘yan bindigar sun fusata ne saboda ‘yan sanda da sojoji sun hana su satar shanu da yawa a ranar Alhamis din da ta gabata."

Ya ce:

“’Yan bindigar sun yi nasarar satar shanun amma rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro ta kama shanun daga hannun su. Haka kuma an kashe wasu daga cikin ‘yan fashin a cikin lamarin.”

Kara karanta wannan

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

Ya bayyana cewa kwanan nan yan sanda suka kona sansanin yan bindiga a yankin wanda mai yiwuwa shine ya fusata yan bindigar.

Mallam Musa ya kuma tabbatar da labarin kwato shanun kuma ya ce hakan na iya zama dalilin kai harin na rashin tausayi.

Ya ce jami’an tsaro a yankin sun yi iya kokarinsu amma ‘yan fashin sun fi su yawa.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar al'amarin ga Channels TV a ranar Lahadi.

Ya ce:

"Eh, gaskiya ne. Lamarin ya faru ne jiya da safe. ‘Yan bindigar sun budewa motar wuta ne domin nuna adawa da kashe daya daga cikinsu da tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin kwamandan Danmusa suka yi musu bayan da suka dakile harin tare da kwato shanu sama da 30 da aka sace.
“Fasinjojin sun kwana a Yantumaki saboda sun isa can cikin dare. Da safe suka hau motar zuwa garin Danmusa inda zasu dauki babura zuwa garuruwansu. An kai wa motar hari ne ‘yan mintoci kadan da barin Yantumaki."

Kara karanta wannan

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

A wani labarin, bayan janye dakarun sojoji daga kauyen Shimfida a karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina, 'yan bindiga sun yi awon gaba da mazauna yankin guda bakwai.

Premium Times ta ruwaito yadda yara bakwai suka rasa rayukan a lokacin da suka yi kokarin yin hijira daga yankin bayan janye dakarun sojojin.

An aje sojojin a makarantar sakandirin gwamnati ta Shimfida, kimanin kilomita 27 daga cikin garin Jibiya, hedkwatar karamar hukuma, har zuwa ranar Alhamis din da aka janye su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel