Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

  • Kasurgumin dan bindiga mai garkuwa da mutane Turji ya nisanta kansa da wata akida ko siyasa
  • Arewacin Najeriya har ila yau na fama da ta'addancin yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Bello Turji na daya daga cikin yan bindigan da suka addabi Arewacin Najeriya musamman jihar Zamfara

Barandanci, ta'addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma.

Jihohin dake fama da matsalar yan bindiga sun hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, da Neja.

A jihar Zamfara kadai, an raba mutane akalla 785,000 da muhallansu.

Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana cewa ba shi da alaka da yan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji
Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji
Asali: UGC

A cewarsa, su basu da wata akida ko ra'ayiin siyasa. Kawai su dau makami ne don kare kawunansu.

A cewarsa:

"Bamu da ra'ayin kafa wata kungiyar addini. Bamu da niyyar yanke wata kasa, kuma babu ruwanmu da siyasa. Mun dau makami ne don kare rayukan al'ummarmu dake kashewa."
"Ba wai bamu da imani bane ko bamu da tsoron Allah ba."

Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji

Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.

Turji ya kara da cewa a rana guda aka kashe masa yan uwa shida bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu.

Haka yasa ya dau bindiga don kare hakkin Fulani yan uwansa da aka takurwa a karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

Amma bisa harkokin kashe-kashe da ya dau alhaki, mutane da dama da basu da hula da gwamnatin sun rasa ayukansu da rayukan yan uwansu sakamakon hare-harensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel