'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu

Katsina - Bayan janye dakarun sojoji daga kauyen Shimfida a karamar hukumar Jibiya na jihar Katsina, 'yan bindiga sun yi awon gaba da mazauna yankin guda bakwai.

Premium Times ta ruwaito yadda yara bakwai suka rasa rayukan a lokacin da suka yi kokarin yin hijira daga yankin bayan janye dakarun sojojin.

'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu
'Yan bindiga sun kwashe mutum 11 a Katsina bayan sojoji sun tattara komatsansu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An aje sojojin a makarantar sakandirin gwamnati ta Shimfida, kimanin kilomita 27 daga cikin garin Jibiya, hedkwatar karamar hukuma, har zuwa ranar Alhamis din da aka janye su.

Shimfida tana daya daga cikin yankunan jihar Katsina da 'yan bindiga ke cin karen su ba babbaka.

A kan lamarin da ya auku ranar Juma'a, wani mazauni yankin, Abdulrazak Ahmad, ya labarta wa Premium Times yadda mazauna yankin guda 11 suka yi kaura daga Shimfida zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira a Jibiya, inda aka yi garkuwa dasu.

Kara karanta wannan

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

Ya ce, yawancin wadanda aka yi garkuwan da su tsoffin mata ne, wadanda ba su bi 'yan gudun hijiran a ranar Alhamis ba.

Haka zalika, wata majiya da ta bukaci sakaya sunanta, ta bayyana yadda mazauna yankin suka ji tsoron sake kai farmakin 'yan bindigan cikin kwanakin nan saboda 'yadda sojoji suka ragargajesu a lokacin da suna nan.

Ya ce, duk mazaunin yankin yayi hijira zuwa Jibiya ko cikin garin Katsina saboda tsoron' yan bindigan.

"Shimfida yanki ne mai tarin arziki. A lokacin da aka aje sojoji a can, hakan bai wa 'yan bindiga dadi ba saboda kasa kai wa yankin hari. Lokaci bayan lokaci su kan yi garkuwa da mazauna yankin, musamman idan sun fita.
"Amma 'yan bindiga basa samun damar kai farmaki saboda sojojin. Amma a lokacin da aka jenye sojojin, mazauna yankin sun ji tsoro, inda suka yanke shawarar yin hijira," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, bai amsa kiraye-kirayen da sakonnin da aka tura mishi ta waya ba a kan aukuwar lamarin.

Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina

A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sako dagaci da sauran mutane 35, bayan biyan N26 miliyan a matsayin kudin fansa, bayan wadanda aka yi garkuwan dasu sun kwashe kwana 29 a hannun 'yan bindigan kafin su sake su a yammacin Lahadi.

'Yan bindiga sun sako dagacin Guga cikin karamar hukumar Bakorin jihar Katsina, Alhaji Umar da sauran mazauna kauyen guda 35 bayan amsar N26 miliyan a matsayin kudin fansa.

Premium Times ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga kauyen a ranar 7 ga watan Fabrairu, inda suka halaka mazauna yankin guda 10 daga bisani suka yi awon gaba da mutane 36, duk da dagacin kauyen.

Kara karanta wannan

Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel