Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

  • Wani dan gwagwarmaya, kuma dan jarida ya bayyana irin azabar da ya sha a hannun Abba Kyari yayin da aka kama shi
  • Ya ce, Abba Kyari ya dauke shi a bayan mota tun daga jihar Legas har Kuros Riba bisa umarnin gwamnan jihar
  • Ya bayyana cewa, gashi shi ma yanzu yana hannu, kuma ya kamata a daure Abba Kyari kamar yadda yake yiwa wasu

Rahoton jaridar Punch ya bayyana yadda dan jarida kuma dan gwagwarmaya, Agba Jalingo, ya sha bakar wahala a hannun Abba Kyari, inda yace ya kulle shi a 'boot' din wata mota daga jihar Legas zuwa Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.

Dan gwagwarmayar, a wani batu da ya fitar a ranar Litinin, ya kuma caccaki jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa kan rashin daure Kyari da sauran wadanda ake tuhuma a kotu ranar Litinin.

Dan jarida ya bayyana wahalar da ya sha a hannun Abba Kyari
Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari tun daga Legas har Kalaba | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A halin da ake ciki dai Abba Kyari na fuskantar tuhuma kan harkallar miyagun kwayoyi tare da wasu jami'ai, inda wasu suka amsa laifinsu shi kuwa Kyari da wasu mutum hudu suka ce sam basu da laifi.

Da yake tsokaci kan bayyanar Kyari a gaban kotu a ranar Litinin, Jalingo ya zargi hukumomin tsaro da baiwa dan sandan damar shan iska.

Alakar Kyari da Jalingo

A 2019 an daure Jalingo na tsawon kwanaki 179 a gidan yarin Afokang da ke Kalaba sakamakon zargin cin amana da gwamnan jihar Kuros Riba, Benedict Ayade ya yi masa.

Daga baya an sake shi a ranar 17 ga Fabrairu, 2020, bisa beli, haka nan SaharaReporters ta ruwaito.

Dan gwagwarmayar a ranar Litinin ya tuna da irin wahalar da ya sha a gidan yari, ya kuma bayyana cewa Kyari da ACP Sunday Ubua (shi ma yana hannun NDLEA) ne suka tuka shi a mota daga Legas zuwa Kalaba a cikin 'boot'.

Jalingo ya ce:

“Gwamnatin Kuros Riba ce ta biya Abba Kyari da ACP Ubua su kamo ni daga Legas, suka tuka ni a mota a cikin boot din wata babbar mota kirar Toyota Highlander suka mika ni Kalaba. Ba zan taba mantawa ba kuma kar ku tambaye ni. "
“An tuhume ni. Duk ranar da na bayyana a kotu, nakan zo ne hannuna dauke da sarka ina daga shi sama.
“A yau, wadannan mutanen sun bayyana a kotu, wadanda suka ji dadin gabatar da wadanda ake zargi cikin farin ciki a bainar kafafen yada labarai, har ma su saba doka, yanzu suna rufe fuskokinsu.
"Rufe fuskokinsu daga me kenan! Kamar yadda suka yi ta nuna fuskokin wadanda suka ajiye kuma suka ki kai su gaban kotu?”

Don Allah kada ku kai mu magarkama: Abba Kyari da 'yan tawagarsa sun roki kotu

A wani labarin, DCP Abba Kyari, wanda ke fuskantar tuhumar safarar miyagun kwayoyi a ranar Litinin a gaban kotu, ya roki babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja da kada ta tsare shi a gidan yari.

Kyari, ta bakin lauyansa, Mista Kanu Agabi, SAN, ya roki kotun da ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a hannun hukumar NDLEA, har zuwa lokacin da za a saurare shi tare da tantance bukatar neman belinsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kyari, wanda a baya yake jagorantar rundunar IRT ta 'yan sanda da aka rushe, ya bukaci hakan ne bayan da ya ki amsa laifuka takwas da NDLEA ta gabatar akansa a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel