Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

  • Rayuka biyar sun salwanta sakamakon mummunan harin da 'yan ta'addan ISWAP suka kai garin Kautikari da ke kusa da Chibok
  • 'Yan ta'addan sun fara shiga anguwar sannan suka wuce kauyen Lassa ke Askira Uba da kauyen Shawa da ke kusa da Chibok
  • Mafarauta ne suka yi kokarin dakile farmakin amma an gano cewa sai da'yan ta'addan suka faraa barna kafin zuwa sojoji

Borno - A kalla rayukan mutane biyar ne suka salwanta a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da mayakan ISWAP suka yi kokarin kaiwa unguwan Kautikari, kusa a Chibok a arewa maso gabashin Najeriya hari.

HumAngle ta ruwaito, kamar yadda wani mazauni yankin ya bayyana, 'yan ta'addan sun doshi anguwan bayan wucewa ta kauyen Lassa a yankin Askira Uba da kauyen Shawa, kilomita kadan daga Chibok, kafin aukawa Kautikari tsakanin karfe 5:00 zuwa 6:00 na yammacin ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari
Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An ruwaito yadda mafarauta suka dakile harin 'yan ta'addan ta hanyar fada da bakin wuta, bayan kai samamen. Sai dai, sun yi nasarar kunna wutar yakin kafin sojojin su iso, gami da fatattakar 'yan ta'addan.

Haka zalika, a watan Janairu, mayakan ISWAP sun hari anguwar wacce take a kudancin jihar Borno, wuren kilomita 16 daga cikin birnin Chibok, kuma kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mayakan ISWAP suna cigaba da cin karen su ba babbaka a yankunan arewa maso gabashin jihar Borno a Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Rayukan dubbannin mutane sun salwanta, bayan mutane sama da miliyan biyu suka rasa gidajen su, saboda rashin zaman lafiya a arewa maso gabashin Najeriya da tafkin Chadi.

Nasrun Minallah: Manyan kwamandojin Boko Haram 50, wasu mayaka 420 sun mika wuya ga sojoji a Borno

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno

A wani labari na daban, jimillar mayakan ta'addanci na Boko Haram da suka mika wuya ga sojojin Najeriya sun kai 470. Daga cikin mayakan ta'addancin akwai manyan kwamandoji hamsin da iyalansu da suka mika wuya ga rundunar Operation Hadin Kai a kudancin jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar da hakan a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne bayan tsananin rugugi da ragargazar da sojin saman najeriya suka yi wa maboyar 'yan ta'addan da matattararsu a yankin tafkin Chadi inda suka halaka mayakan ta'addan masu tarin yawa.

Daily Trust ta tattaro cewa, 'yan ta'addan sun fito daga dajin Sambisa a ababen hawa kusan goma inda kai tsaye suka tunkari sansanin sojoji da ke Gwoza, hedkwatar karamar hukumar Gwoza ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel