Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

  • Yan bindiga sun farmaki cocin Salama Baptist Church da ke kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Maharan sun yi awon gaba da limamin cocin da wasu mutane bakwai da ke tsaka da ibadah
  • Lamarin wanda ya afku a safiyar yau Lahadi na zuwa ne yan sa'o'i kadan bayan farmakin da mahara suka kai wasu kananan hukumomin jihar inda suka kashe mutum 17

Niger - Yan ta’adda sun yi garkuwa da akalla mutane takwas a yayin da suke yin ibadah a cocin Salama Baptist Church da ke kauyen Gidigori a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Wata majiya daga garin ta ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja
Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewar limamin cocin na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Rahoton ya kuma kawo cewa cocin na kusa da yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin na zuwa ne yan sa'o'i kadan bayan wasu miyagun 'yan ta'adda sun farmaki kauyukan kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi dake jihar Niger inda suka kashe akalla mutane 17.

An tattaro cewa ama'a da yawa sun yi ta barin gidajensu sakamakon farmakin wanda ya auku daga karfe 12 na rana zuwa karfe takwas na ranar Asabar.

A karamar hukumar Mashegu, kauyukan da aka kai hari sun hada da Sabon-Rami, Igbede, Chekaku, Ubegi, Maishankafi da Poshi.

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

A wani labarin kuma, mun kawo cewa mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP sun kashe akalla mutane takwas a wani hari da suka kai karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa

Jaridar The Cable ta rahoto cewa mayakan sun farmaki kauyukan Mandaragirau da Ghuma da ke karamar hukumar a daren ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, inda suka kashe mazauna takwas da kuma jikkata wasu.

An tattaro cewa wasu majiyoyi na rundunar soji ta dakile wani hari da ISWAP suka kai hanyar Mandaragarau a safiyar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel