An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

  • Rayuka 18 ne suka salwanta a kauyen Kadaddaba da ke karamar hukumar Anka sabon farmakin da miyagu suka kai
  • Mazauna yankin sun ce miyagun sun kwashe sa'o'i shida suna barin wuta inda suka gida-gida tare da kwace abinci, kudi da dabbobi
  • An tabbatar da cewa wadanda suka yi yunkurin barin garin ko kuma masu taurin kai ne 'yan ta'addan suka halaka

Zamfara - A kalla rayuka 18 ne suka salwanta yayin da wasu masu yawa suka raunata bayan farmakin 'yan ta'adda a Kadaddaba da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, farmakin ya kwashe kusan sa'o'i hudu tunda 'yan ta'addan sun bayyana wurin karfe goma na dare ne kuma suka kai har hudun asuba kuma shi ne na farko da aka taba kai wa kauyen.

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18
An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kilomita kadan ke tsakanin kauyen Kadaddaba da kwalejin gwamnatin tarayya ta Anka, wacce ba ta da nisa da garin Anka.

'Yan ta'adda sun sha kai farmaki kauyukan yankin inda suke sace mutane sai an biya kudin fansa tare da satar shanu na tsawon shekaru a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan bindigan sun halaka sama da rayuka dari biyu a daya daga cikin miyagun farmakin da suka kai a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Wani mazaunin garin Anka mai suna Ibrahim Danda, ya sanar da Premium Times ta waya cewa 'yan bindigan sun tsinkayi garin a sabodan farmakin a kan babura.

"Daga abinda na tattaro, 'yan bindigan sun kewaye dukkan kauyen yayin da wasu suka shiga. Sun shiga gida-gida inda suka dinga karbar kudi, kayan abinci, dabbobi kafin su fara harbe-harbe babu kakkautawa.

"Wasu mazaunan kauyen da suka tsere zuwa garin Anka sun ce wadanda aka kashe suna daga cikin masu taurin kai ko kuma tserewa," yace.

A kan batun mutum nawa suka halaka, Danda wanda lauya ne, ya ce mazauna kauyen sun birne mutum goma sha shida a safiyar Asabar bayan 'yan ta'addan sun tafi, akwai wasu mutum 2 kuma da ke babban asibitin Anka.

Wani mazaunin garin Anka mai suna Ansar Aliyu, ya ce ya ji harbe-harbe a yankin yayin da ake kai farmakin.

"Na fara jin harbin bindiga wurin karfe 11 na dare kuma duk da bansan wanne gari suka je, na san cewa ta yankin Kadaddaba suke, Da safe liman ya sanar a masallaci cewa can suka kai farmaki."

An kasa samun Mohammed Shehu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar domin yayi tsokaci kan lamarin.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka sama da rayuka talatin, sun yi garkuwa da wasu mata a hari mabanbanta a ranar Juma'a duka a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.

Yankunan da aka kai farmakin sun hada da Nasarawar mai Fara da ke karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina a karamar hukumar Bungudu da kauyen Nasarawa da ka karamar hukumar Bakura.

Zamfara kamar sauran jihohin arewa maso yamma, ta na fama da rashin tsaro. Al'amuran 'yan bindigan kullum kara kamari su ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel