'Yan Najeriya a Ukraine: Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari a madadin 'yan Najeriya

'Yan Najeriya a Ukraine: Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari a madadin 'yan Najeriya

  • Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, ta tabbata uwa ga 'yan Najeriya
  • Uwargidan shugaban Najeriya ta yi kira da a yafe kudin gwajin Korona ga duk 'yan Najeriyan da suka dawo daga Ukraine
  • Aisha a wani sakon da ta wallafa a Facebook ta kuma yi kira ga fadar shugaban kasa da ta soke karbar kudin ga yaran kasar da za su dawo gida Najeriya nan gaba

Kokarin da jami’an diflomasiyyar Najeriya ke yi na ganin an kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Ukraine da yaki ya dumfara ya sha yabo daga Aisha Buhari.

Sai dai, a cikin wani sakon da ta wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, uwargidan ta shugaban Najeriya ta yi kira ga kwamitin shugaban kasa kan yaki da Korona da ta yafe kudin gwajin Korona ga 'yan Najeriyan da suke dawowa daga kasashen Turai.

Kara karanta wannan

Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce

Uwargidan shugaban kasa ta magantu kan yanayin 'yan Najeriya a kasar waje
Game da 'yan Najeriya da ke Ukraine: Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari | Hoto: Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

Ta kuma roki a soke karbar irin wadannan kudade ga duk yaran Najeriya da ke dawowa gida nan ba da dadewa ba, tare da rage kudin gwajin ga dukkan ‘yan Najeriya.

A kalamanta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na yi farin cikin samun labarin kokarin da jami'an diflomasiyyarmu ke yi na saukaka dawowar 'yan kasarmu da ke makale a kasar Ukraine cikin koshin lafiya.
“Ina rokon Shugabancin Kwamitin Shugaban kasa kan yaki da cutar Korona da su cire kudin gwajin Korona a madadin dawowarsu, tare da soke irin wannan kudi ga duk yaran da ke shirin dawowa gida tare da rage kudaden gwajin ga dukkan ‘yan Najeriya."

Ba wannan ne karon farko da Aisha Buhari ke aika sako ga gwamnatin Buhari ba game da halin da 'yan Najeriya ke ciki.

Ta kafa tarihi: A karon farko Aisha Buhari ta kai ziyara zauren majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

A wani labarin, uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari ta yi tattaki, inda ta kai ziyarar gani da ido a zauren majalisar dokokin kasar nan, inji The Nation ta ruwaito.

Ziyarar da Aisha Buhari ta kai zaurukan majalisun ya zama babban tarihi tun kafuwar Najeriya, domin kuwa a kanta aka fara haka, ita ce matar shugaban kasa ta farko da taba kai ziyara zauren majalisar dokoki.

Ta kasance a zauren majalisar ne don shaida azamar majalisa a rahoton kwamitin duba gyara ga kundin tsarin mulki na majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel