Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce

Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce

  • Wani bidiyo dake nuna gidan man da ake yawo da shi kan titin Dubai ya jawo cece-kuce a yanar gizo
  • Bidiyon da wani dan Najeriya ya dauka a dubai, wanda ya kushe kasar shi, ya siffanta UAE a wurin da abubuwa ke aiki
  • Dan Afrikan dake zaune a kasar ya kara da cewa, a gida Najeriya hakan nan mutum ke hukuri da daukar tsawon lokaci yana bin layin siyan man fetur

Wasu 'yan Najeriya sun sha mamaki, bayan ganin wani bidiyo da yayi ta yawo a kafafan sada zumuntar zamani na gidan man da ake yawo dashi a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.

Hakan yazo ne daidai da lokacin karanci da tsadar man fetur. Ya yi suka ga Najeriya saboda rashin cigaba ta wannan fannin.

Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce
Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce. Hoto daga @instablog9ja
Asali: Instagram

Dan Najeriyan da ya dauki bidiyon da @instablog9ja suka wallafa a Instagram, ya jinjina wa kasar UAE a matsayin wurin da abubuwa ke aiki.

Kara karanta wannan

Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai

Ya kushe Najeriya, inda ya ce, mutane suna tsayawa kan layin a gidajen mai, har da su bada cin hanci kawai don su samu man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A guntun bidiyon da ya wallafa, an ga wani ma'aikacin gidan man da ake yawo dashi yana sallamar kwastoma da dare a titin Dubai. Babu bukatar kwastomar ya bar motar shi, ma'aikacin ke yin duk aikin.

'Yan Najeriya sun yi martani

Ga wasu daga cikin tsokacin mutane a kan bidiyon.

@chocodami___ ta ce: "komai a Najeriya ci baya ne mxwww man fetur da muke samar wa yanzu yayi karanci."
@cjidoxflash yayi tsokaci : "kasashe na cigaba da bunkasa. Ba kamar nan ba. Inda babu abunda ke faruwa."
@phyzee07 ya tofa nashi albarkacin: "Amma a nan, gwamnati tana tunanin ta yi kokari sosai da yin titina. Sun mai da shi siyasa."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

@sammysteve_yayi tsokaci: "Yan Najeriya suna kaunar yin tsokaci a duk abunda suka gani a kasar wani. Ku kwantar da hankalin ku mana."

Saudiyya za ta ci tarar SAR 2000 kan duk wanda ya kunna waka yayin kiran sallah a kasar

A wani labari na daban, gwamnatin Saudi Arabia sun kara gyara dokoki ga mahajjata a Makkah da Madinah ta hanyar samar da sabbin matakai, wanda aka gabatar wa al'umma a ranar Asabar.

Kamar yadda gwamnatin ta fada, mahajjatan da suke tahowa daga masarautar ko daga sauran kasashe, ana ganin su na amfani da ababen hawa yayin kiran sallah ( Adhan), wanda hakan bai dace ba, kuma haramun ne, The Islamic Information ta ruwaito.

Saboda haka ne, hukumomin Saudi suke jan kunnen al'umma a kan wasa ko kara sautin waka a cikin gidajen dake anguwanni yayin Adhan da Iqamah ( kiran sallah na farko da na biyu).

Kara karanta wannan

Reels: Meta ya kirkiri hanyar da masu hawa Facebook za su ke samun na kashewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel