Ta kafa tarihi: A karon farko Aisha Buhari ta kai ziyara zauren majalisar dattawa

Ta kafa tarihi: A karon farko Aisha Buhari ta kai ziyara zauren majalisar dattawa

  • Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta kai ziyarar gani da ido a majalisar dokokin tarayyar Najeriya
  • Ta kai ziyara majalisar dattawa, kafin daga bisani ta zarce zuwa majalisar wakilai tare da mukarrabanta
  • Shugaban majalisar dattawa, da kuma kakin majalisar wakilai ne suka sanar da ziyarar a yau Laraba

FCT, Abuja - Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari ta yi tattaki, inda ta kai ziyarar gani da ido a zauren majalisar dokokin kasar nan, inji The Nation ta ruwaito.

Ziyarar da Aisha Buhari ta kai zaurukan majalisun ya zama babban tarihi tun kafuwar Najeriya, domin kuwa a kanta aka fara haka, ita ce matar shugaban kasa ta farko da taba kai ziyara zauren majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Majalisar dokokin Zamfara ta tsige mataimakin gwamna daga kujerarsa

Majalisa ta shaidi ziyarar matar Buhari
Kafa tarihi: A karon farko Aisha Buhari ta kai ziyara zauren majalisar dattawa
Asali: Original

Ta kasance a zauren majalisar ne don shaida azamar majalisa a rahoton kwamitin duba gyara ga kundin tsarin mulki na majalisar dattawa.

Majalisar dattawa ta dage gabatar da rahoton zuwa wani dan lokaci a yayin gudanar da aikin domin baiwa Aisha Buhari damar zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Uwargidan shugaban kasar ta samu rakiyar ministar harkokin mata Mrs Pullen Tallen; Ministar kudi, tsare-tsare ta kasa, Mrs Zainab Ahmed da wasu mataimakanta.

Ta ziyarci zauren majalisar wakilai

Har ila yau, Aisha Buhari ta gangara zuwa majalisar wakilai, inda kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya sanar da isowar uwargidan shugaban kasar.

Sanarwar da majalisar ta fitar yayin zaman majalisar ta shafin Twitter ta ce:

"Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta kawo ziyara a zauren majalisar wakilai. Misis Buhari ta kawo ziyarar gani da ido kan yadda ake tafiyar da harkokin majalisa."

Kara karanta wannan

Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa

Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC 6, ya kuma jagoranci zaman majalisar zartarwa

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu.

Dan takaitaccen taron wanda ya gudana a zauren majalisar fadar shugaban kasa, ya samu halartan shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma shugaban INEC, Mahmood Yakubu.

Kwamishinonin INEC shida da aka rantsar sune Mallam Mohammed Haruna daga jihar Neja, Misis May Agbamuche-Mbu daga Delta, Ukaegbu Kenneth Nnamdi daga jihar Abia, Manjo Janar A. B Alkali mai ritaya daga Adamawa, Farfesa Rhoda Gumus daga jihar Bayelsa da kuma Mista Sam Olemekun daga jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel