Buhari: Ba Domin Ni Ba, Da Mutane Sun Riƙa Taka Wa Daga Legas Zuwa Abuja

Buhari: Ba Domin Ni Ba, Da Mutane Sun Riƙa Taka Wa Daga Legas Zuwa Abuja

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara yaba wa kan sa inda yace da bai sanya hannu ba da har yanzu ba a kammala ayyukan hanyoyin sufurin Legas zuwa Ibadan ba, a cewarsa da yanzu da kafa jama’a suke zuwa Abuja daga Legas a kasa
  • A ranar Talata Buhari ya ce jajaircewa akan kammala ababen more rayuwa ya samar wa wasu yankunan saukin rayuwa musamman kammala titina da hanyar jiragen kasa daga Ibadan zuwa Legas
  • Shugaban kasa ya shaida wa wakilan da suka kai masa ziyara daga Kaduna wadanda sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balaraba suka yi jagora

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara yaba wa kansa inda ya ce in baya ga ya sanya hannu, da yanzu ba a kammala ayyukan hanyoyin Legas zuwa Ibadan ba, da yanzu jama’a suna takawa a kasa daga Legas zuwa Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Talata inda ya ce mayar da hankali kan ababen more rayuwa a wasu yankunan da ke kasar nan, musamman wurin kammala hanyoyin jirgin kasa da titinan Legas zuwa Ibadan ya kawo saukin cunkoso.

Buhari: Ba Domin Ni Ba, Da Mutane Sun Rika Taka Wa Daga Legas Zuwa Abuja
Ba Domin Ni Ba, Da Mutane Sun Rika Taka Wa Daga Legas Zuwa Abuja, Buhari. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kamar yadda shugaban kasan ya fadi yayin da wasu wakilai daga Jihar Kaduna wadanda Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Hadiza Sabuwa Balaraba suka kai gidan gwamnatin.

Buhari ya ce babu kasar da ta ci gaba idan babu ababen more rayuwa

A cewarsa:

“Ya kamata a yi dubi da ababen more rayuwar da muka samar. Babu kasar da zata ci gaba babu ababen more rayuwa. Akwai lokutan da akwai hanyoyin jirgin kasa, musamman mutanen kudancin Kaduna zasu tuna da wannan lokacin.

Kara karanta wannan

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

“Wacce kasa ce zata ci gaba babu titina, hanyoyin jirgin kasa da wutar lantarki? Wannan tunanin yasa na bukaci in inganta ababen more rayuwa musamman yadda kowa ya san ‘yan Najeriya da kujiba-kujiba don harkokin kasuwancin su.”

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, shugaban kasa ya ce hanyoyin zuwa kudu maso yamma sun gyaru. Mutanen kudu maso yamma ne zasu fi tantancewa saboda hanyar Legas zuwa Ibadan ta gyaru.

Ya yi godiya ga mutanen China da suka tallafa wurin gyaran hanyoyin jirgin kasa

A cewarsa:

“In banda mun sa hannu, da yanzu babu titina, hanyoyin jiragen kasa da ga kuma matsalolin rashin tsaro mai yawa. Da yanzu jama’a a kasa suke takawa.
“Muna godiya ga mutanen kasa da kasa. Mun gode wa mutanen China wadanda suka zo musamman suka sa hannu wurin gyaran hanyoyin Legas zuwa Ibadan.”

Shugaban kasa ya yaba wa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, akan yadda ya gyara Jihar Kaduna ta hanyar inganta ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

Ya bukaci wakilan su mika godiyarsa ga gwamnan Jihar Kaduna akan kokarinsa wurin gyara jiharsa. Buhari ya ce ya dade yana zama a Kaduna amma yanzu ko ina ya sauya mishi.

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel