Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

  • Bayan kwanaki da kisan yan Arewa mas sayar da dabbobi a jihar Abia, gwamnatin Adamawa tayi sabuwar sanarwa
  • Sakataren gwamnatin jihar yace daga yanzu zasu fara hana kai dabbobi kudu don sayarwa
  • Gwamnatin Yola tace dalilin yin hakan shine zaluncin kudaden da ake karba hannun masu kai dabbobin

Jimeta - Gwamnatin jihar Adamawa ta yanke shawarar hana kai Shanu yankunan kudu saboda toshe yoyon kudaden shiga da kuma ingantashi ta hanyar kaiwa wasu jihohi.

Sakataren gwamnatin jihar, Bashir Ahmad, ya yi bayanin wannan sabuwar dokar.

Yace gwamnatin jihar ta yanke shawarar hana kai Shanu wasu jihohin kudu cikin har da Legas saboda suna karban harajin N35,000 kan shanu guda.

Gwamnatin jihar Adamawa
Zamu hana kai Shanu jihar Legas, dss: Gwamnatin jihar Adamawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

A cewarsa, hana kaiwa yankunan zai taimakawa tattalin arzikin gida.

Yace:

"Abinda muke karba matsayin harajin Shanu bai kai abinda ake karba hannun masu kaiwa kudu ba a hanya."
"Mutane kan kai Shanu Legas daga Mubi, amma a hanya suna biyan N,5000 kan kowani shanu, kuma ana karba kimanin sau biyar kan su isa."
"Idan suka isa Legas su sayar, zasu sake biyan N10,000 kafin a iya yanka Saniya, amma a nan Adamawa da sai da mu samu N300 zuwa N500."

Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

Wannan ya biyo bayan harin Yan bindiga inda suka kashe mutane da dama a yayin wani farmaki da suka kai sabuwar kasuwar shanu ta Abia da ke Omumauzor, karamar hukumar Ukwa West da ke jihar Abia.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun kai farmakin ne a daren ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

An tattaro cewa harin tsakar daren ya sanya mazauna kauyen cikin halin firgici da tsoro.

Rahoton ya kuma kawo cewa jami’an tsaro sun karbe yankin domin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel